Babban bankin kasar Sin ya zayyana muhimman batutuwan da suka shafi kudi wadanda za a ba da fifiko a shekarar 2025, bayan wani taron yini biyu da aka kammala a jiya Asabar, inda ya jaddada fadada bukatun cikin gida, da daidaita hasashe da kuma kara kuzari don tabbatar da ci gaba mai dorewa a tattalin arzikin kasar Sin.
Bankin jama’ar kasar Sin wato PBOC a takaice, ya bayyana cewa, zai aiwatar da tsarin hada-hadar kudi mai sassauci a shekarar 2025, da dakile hadurra masu alaka da hada-hadar kudi a muhimman fannoni, da kara zurfafa yin gyare-gyare a harkokin kudi da inganta bude kofa ga kasashen waje.
- Babban jami’in JKS Ya Yi Kira Da A Nazarci Kuma A Aiwatar Da Tunanin Xi Jinping Kan Al’adu
- Japan Ta Bai Wa Nijeriya Bashin Dala Miliyan 108 A Matsayin Daukin Gaggawa Don Samar Da Abinci
Da yake kaddamar da manufofin hada-hadar kudi na bana, babban bankin kasar Sin ya bayyana cewa, zai aiwatar da tsarin kudi mai sassauci don samar da ingantacciyar yanayin hada-hadar kudi don daidaita ci gaban tattalin arziki.
Har ila yau, ya bayyana yin amfani da salon gaurayar manufofi don rage kason kudaden da hukumomin harkokin tattalin arzikin kasar ke ajiye a babban bankin kasar bisa jimlar kudaden da aka ajiye a cikinsu da kuma yawan kudin ruwa a lokacin da ya dace, bisa la’akari da yanayin tattalin arziki da hada-hadar kudi na cikin gida da na duniya, da kuma yadda ake gudanar da kasuwannin hada-hadar kudi.
PBOC ya ce, zai ci gaba da samar da isassun kudade na hada-hada da kuma kara samar da kudade a kai a kai, ta yadda karuwar bukatun kudi na jama’a da kudaden da ake samarwa za su yi daidai da abin da aka sa a gaba na ci gaban tattalin arziki da matakan farashi gaba daya. (Mohammed Yahaya)