Shafi ne da ya saba zakulo muku fitattun jaruman finafinan Hausa manya da kanana, wadanda suka jima ba a san su ba, har ma da masu tasowa a yanzu.
Kamar kowane mako, yau ma shafin na tafe da daya daga cikin masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, wanda ya shafe tsahon shekaru masu yawa, cikin masana’antar, Wato MURTALA MUHAMMAD ABDULLAHI, wanda aka fi sani da MURTALA M. SHUGABA, inda ya baje wa masu karatu batutuwa masu yawan gaske, wadanda suka shafi sana’arsa ta fim, har ma da ita kanta masana’antar Kannywood din baki daya.
Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA kamar haka;
Da farko za ka fara fada wa masu karatu cikakken sunanka tare da sunan da aka fi saninka da shi.
Sunana Murtala Muhammad Bajin, a makaranta kuma Murtala Muhammad Abdullahi, a harkar finafinan Hausa ana ce min Murtala M. Shugaba, wasu kuma su ce min Darakta.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
An haife ni a Garin Zangon Barebari ta Karamar Hukumar Ungoggo, unguwar Kanawa gidan Alhaji Bajin wanda aka fi sani da gidan maharba. Daga nan aka yaye ni aka kai ni Fanisau bayan gidan sarki, sai aka kara dawo da ni Zangon Bare-bari. Daga nan aka kara dauka na aka kai ni Gwammaja gidan wan babata, a Gwammaja na fara. makarantar Allo. Daga nan aka ga karatun nawa kamar ba ya tafiya sosai, sai aka kai ni Jigawa Birnin Kudu can wani kauye da ake kira Bodinga. A can Kauyen akwai wani tsangaya da ake kira Tsangayar Tudu wacce take a Hayin Ruwa, a can na yi karatun Allo. Bayan nan aka ga ya kamata mu tafi rani, sai aka kai ni wani gari a Jigawa ana ce masa Basruka, a gidan wani mutum da ake kiransa Dogon Dawa, a can na ci gaba da karatun Allo. Ina karatun Allo ina kamun kifi (Suu). Mun dawo Bodinga da karatun Allo, muna ‘Suu’, muna farauta, muna itace, mu zo mu ci da kanmu da sauransu, lokacin don ba a fiya bara sosai ba. Daga baya na dawo gida Zangon Bare-bari, zaman shi ma ya gagara, sai na koma Gwammaja bayan gidan Malam, layin manga mai kifi. Aka saka ni a makarantar firamare ‘Gwammaja Special Primary School’, daga nan na ci makarantar ‘Gwammaja 1’, na kammala sakandare na. Daga nan kuma na fara gyaran Agogo, sai aka yi min nasiha na koma makaranta. Wani yayana Nura Muhammad Bajin ya takura na koma makaranta na karasa karatuna na sakandare. Daga nan na tafi ‘School of Hygiene’ har na kammala, sai na fara HND, sai na samu ‘Problem’ na ‘Rekuirement’ suka dawo da ni EBT shi kuma Diploma ne sai na karasa, bayan na karasa na koma HND.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood?
Ni ba shiga Kannywood na yi ba, Kannywood din ce ta zo ta same ni a Kano, sai muka zama Kannywood. Na girmi Kannywood gaskiyar magana, mu a ‘da’ ‘yan kungiyoyi ne kawai, to, ina ciki aka kirkiri Kannywood.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara Dirama?
Na fara Dirama a lalace tun 1993, duk wadannan ‘yan wasan da ku ka sani irin su; Ali Nuhu, su Sadik Sani Sadik, Tijjani Hassan, Sani Ibrahim, Gidigo, da sauransu duk mun san lokacin da suka shigo.
Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?
Tun ina firamare na tsunduma harkar fim, a lokacin ana yin wasan Dabe ne to, tun ina karami na fara wasan dirama daga 1992 zuwa 1993. A 1994 aka fara dora min ‘Kyamara’ lokacin ina ‘Kungiya’ namu na kanmu da muka kirkira. Daga nan sai na tafi wani ‘kungiya’ da ake ce mata ‘Line monkey’ ma’ana kamar wasan China kenan. Da ta ruguje sai na koma wani kungiya a Kofar Ruwa mai suna ‘Black Tea’ na dai manta sunanta, na fara wasa wajen su Master Abdulkadir, daga nan na ga iyawani ya wuce saninsu.
Sai na ji labarin wani kungiya mai suna ‘Dabo’ don a wancen lokacin duk wanda bai yi Dabo ba za a rika kallonsa kamar bai yi wani babban kungiya ba. Na shiga ta hannun su Kabiru na Kongo, Kabir me holder, Malam Inuwa, muka rika wasanni na china da sauransu.
Daga nan muka samu matsala da Dabo, sai aka ce mu tara (9) an dakatar da mu, ba za a dawo da mu ba har sai baba ta gani. Daga nan wani kungiya ‘Nasiha’ suka ji labari suka dauke ni, suka raine ni na karbi horo ba dare ba rana. Kwatsan sai suka zo za su yi fim, a takaice mu ne muka fara saka Sani Mai Iska mijin Fati a fim ‘A Duniya’.
Daga nan muka yi wani fim ‘Gaskiya Ta Kori Karya’ ni ne jarumi a fim din, lokacin ina koyan ba da imarni a Dabo, ba ilimi na koyi bada umarni a lokacin. Da sassafe nake zuwa na koma gefe na yi tsuru, lokacin su Kabiru Nakango da su Nuhu Me walda su Kasko, Masani dul shugabanni na ne, ina ji suna a yi ka-za ina ta nadewa idan na koma sai na rika jarabawa, lokacin ma babu waya. Daga baya na koma wasan Dabe da aka zo lokacin shari’a sai kwankwaso ya hana duk wasan Dabe, shi ne na koma bada umarni na finafinan Hausa.
A wancen lokacin ko akwai wani kalubale da ka fuskanta a gida, ta dalilin shigar ka wasan Dabe?
Ai gidan ma duk suna so, lokacin da za a yi bikin wani babbar yayarmu Umma, sai na gayyato ‘yan China aka zo aka rika yi min liki ‘yan uwa da dangi muna wasa. Duk da dai a wasan ni ake yi wa duka, amma ni ake yi wa liki.
Bayan kirkirar Kannywood da aka yi a lokacin da ka ke tsaka da wasan Dabe, ta yaya ka rikida daga wasan Dabe zuwa kannywood, ko kuwa ku din ne ku ka zama Kannywood din?
Kamar yadda na fada, Kannywood ta same mu ne a ciki, idan muke a ‘Dabo Film Association’ su ne farkon Kannywood din, kuma su ne farkon kungiyoyi masu yin finafinai a Hausa fim, kuma muna ciki. Na yi aikace-aikace na finafinai irin su; Na yi haska wuta, Kwalliya, bada kayan costume, da sauransu. Duk wani abu da ake yi na yanzu a harkar fim, kusan gaskiya duk na yi su. Sannan na rikida na zama ‘Producer’ na koma darakta, har ‘kyamara’ na yi.
Bayan ka rikida ka zama dan Kannywood a wancen lokacin, wane bangare ka fi mayar da hankali a kai cikin abubuwan da ka yi wanda ka lissafo?
Na fi mayar da hankali ga wasan canis, saboda shi ne ya koma ‘Action’. Wannan ya sa a yanzu haka idan za a yi finafinai na fada to, ana iya gayyato ni na zama ni ne darakta. Kamar irin fim din Madugu na ‘Sulta film factory’, kusan ina cikin wadanda suka yi bada umarni na ‘action’ na fada. Sannan akwai wani fim na Baballe Hayatu shi ma ni ne na yi bada umarni na fada mai suna ‘Shuka’ da dai sauransu. Duk dai wani fim idan za a yi da ‘action’ ana kira na sai na je na yi bada umarni iya wajen damben.
Idan na fahimce ka kana so ka ce, kana bada umarni iya fada ne ba wai fim gabadaya ba kenan?
A’a! Ba iya fada kadai nake bada umarni ba, ni fim darakto ne, ina cikin kungiyar daraktoci ma na Kano gabadaya. Ina bada umarni na fim, ina da finafinai da nake bada umarni yanzu haka kamar fim din; Kasuwar
ka kawo masana’antar, ko akwai wadanda suka shahara duniya ta san da zamansu?
Eh! akwai irinsu; Amina Fulani, Safara’u wacce ta auri Adamu Zango ita ma ni na kawo ta. Akwai; Sadam, Dan’Hisba, Aminu Mister Man, suna da yawa gaskiya akwai; CP ontop, akwai Rukayya wacce ta fito a cikin Garwashi, Anti Asiya wacce ta fito a Adaman Kamaye, suna da yawa gaskiya.
A yanzu, ka taba fitowa matsayin jarumi, ko kuma a rasa jarumin da zai taka rawa ka maye gurbinsa, ko kuwa iya ayyukanka kawai ka tsaya?
Eh! Na taba fitowa a jarumi kamar Zafin Nema da ake haskawa a yanzu, ba fim na je yi ba na je na bayar da kauye ne kuma na bayar da mutane. Na fito a Sallau mai nama.
Ya kake kallon yadda fitowarka ta kasance da kuma sauran ayyukanka, shin yanzu za ka ci gaba da taka rawa matsayin jarumi tare da ayyukanka ko kuwa iya zafin nema za ka tsaya?
Daman ina taba aiki kala-kala, amma dai gaskiya ban taba saka kaina yin wannan rol din ba babba gaskiya, zan ji tsoron kar na je na fadi.
Mene ne burinka na gaba game da fim?
Burina na gaba mu rika kokarin bunkasa yare, da addini, da kuma al’adu masu kyau na Hausa.
Bayan fim kana wata sana’ar?
Ina harkar lafiya, sannan kuma ina yi wa yara ‘Edtra Lesson’ Asabar da Lahadi. Sannan kuma sai rentin na kayayyaki da shaddodi, sai kuma kiwo da sauransu.
Kana nufin aikin asibiti kenan?
E, da ne nake asibiti, amma yanzu ba na aikin asibiti, fim ya janye hankalinmu gabadaya. Duk da dai an ba ni shawara, tun da na ga na yi fim daya na samu dubu dari, na ce na daina wata sana’a in ba fim ba. An ba ni shawara amma ban ji ba na rika finafinai na.
Ya batun iyali, shin akwai ko babu?
E, akwai iyali. Ina da ‘ya’ya na guda uku, Zainab, Bintul-Huda, da kuma Khairiyya. Sannan kuma har ma guda ukun suna fim, ina da ‘ya ta ‘yar wani biyu yanzu haka tana wani fim ‘Shuda’ na Mansura Isah, ‘ya ta Zainab ta fara fim ita ma, sai Bintu-huda ita ma ta fara fim.
Kana da ra’ayin su cigaba da yin fim har girma, ko kuwa akwai wani geji da idan sun kai za ka dakatar da su?
Ni a tsarina yarinyata Bintul Huda, idan ta kai shekara tara to, duk aikin da za ta yi ba tada lokacin makaranta. Sai idan kamfani na ne tun da ina yawan finafinai zan rika saka ta, ko fim dina ne sai an yi hutu sabida makaranta.
Mene ne ra’ayinka game da auren ‘yar fim?
Za a iya auren ‘yar fim mana ba matsala, ni kaina idan zan yi aure zan iya auren ‘yar fim ba wani abu bane, ai daman shi aure ana duba tarbiyya ne, da dangi da sauransu.
Wane sako ka ke da shi ga masoyanka, masu kallon shirye-shiryenka?
Muna godiya gare su, da fatan alkhairi, kuma muna kara rokonsu idan akwai matsaloli da kura-kurai a fada mana ta lambobin wayar mu.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Ina gaida Master Ashiru da Tahir I. Tahir maigidana, da kuma Sultan Film Factory masoyina kuma abokina, da Dan’duniya da kuma Hajiya Zulai Bebeji, da Baballe Hayatu, da maigida na kuma Daraktana Hafizu Bello.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp