Hukumar yaƙi da cin Hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana tsohon ƙaramin Ministan Harkokin Man Fetur, Timipre Sylva, a matsayin wanda ake nema kan zargin yin zamba da satar kuɗi har dala $14,859,257.
EFCC ta ce kuɗin wani ɓangare ne na kuɗaɗen da hukumar ci gaban albarkatun Nijeriya (NCDMB) ta saka a kamfanin Atlantic International Refinery and Petrochemical Limited domin gina wata matatar sarrafa mai.
Sylva, mai shekaru 61, ɗan asalin ƙaramar hukumar Brass ta jihar Bayelsa ne. Sanarwar ta EFCC ta ce wannan mataki ya biyo bayan umarnin kotun babban birnin Lagos na ranar 6 ga Nuwamba, 2025.
Hukumar ta roƙi duk wanda ke da bayanai kan inda Sylva yake da ya tuntuɓi EFCC a kowane ofishin ta na jihohi da ke Ibadan, Uyo, ko Sokoto, Maiduguri, ko Benin, ko Makurdi, ko Kaduna, ko Ilorin, ko Enugu, ko Kano, Lagos, ko Gombe, ko Fatakwal ko kuma Abuja.
LEADERSHIP ta rawaito cewa Sylva, tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, kwanan nan an danganta shi da wani zargin shirin juyin mulki, yayin da kakakinsa ya amince da cewa jami’an tsaron DIA sun ziyarci gidansa na Abuja.













