Wasu ƴan kasuwa da dama a kan titin IBB, cikin birnin Kano, sun rufe kasuwancinsu ba zato ba tsammani, don bin abokan kasuwancinsu zanga-zangar adawa da sanarwar korar su a inda shagunansu suke.
Majiyoyi sun ce gwamnatin jihar na shirin rusa shaguna da rumfunan da ke yankin wanda hakan ya haifar da hargitsi yayin da ƴansanda suke sintiri a yankin suna harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa ƴan kasuwa da sauran jama’a.
- Sarkin Kano Na 15 Ya Umarci Hakiman Da Ke Goyon Bayansa Su Halarci Hawan Sallah
- Rusau: ‘Yan Kasuwar Kano 5,000 Za Su Rasa Shagunansu Bayan Shafe Shekaru 18 A Kasuwa
A ranar Litinin ne hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano, KNUPDA, ta ba ƴan kasuwar sa’o’i 48 da su bar yankin.
Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar, Yakubu Muhammad, ya ce hukumar KNUPDA ta bayar da sanarwar ne ga ƴan kasuwar da shagunansu ke kusa da wajen da aka rusa shekarar da ta gaba ta, kusa da filin Sallar Idi.
Malam Muhammad ya ce tun sama da shekaru 18 Majalisar Masarautar Kano, ta raba musu wurin bisa shawarar Marigayi Galadiman Kano Tijjani Hashim, inda daga baya gwamnati ta tsara yadda za a raba musu shaguna da rumfuna.
Sai dai kawo yanzu gwamnatin jihar Kano ba ta ce uffan kan lamarin ba.