Duk da sauke shi da gwamnatin jihar Kano ta yi a ranar 23 ga watan Mayu, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya umurci hakimai da su halarci Hawan Sallar Idi a Kano a ranar 16 ga watan Yuni.
Wata wasiƙa daga babban mashawarcin fadar Alhaji Abbas Sunusi ce ta umurci hakiman da su shirya halartar fadar Nassarawa domin hawan Sallah.
Boko Haram Sun Sace Fasinjoji A Kan Hanyar Maiduguri Zuwa Kano
‘Yan Jarida Sun Dakatar Da Kawo Rahotanni Daga Fadar Gwamnatin Kano
Bayan sauke shi sakamakon soke dokar Masarautar ta 2019, Alhaji Aminu Ado Bayero na ci gaba da zaman jiran umarnin kotu na mayar da shi a fadar Nassarawa ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.
A halin da ake ciki kuma, Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi II, yana babbar fadar mulkin Kano da ke Gidan Rumfa.