• English
  • Business News
Saturday, September 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Babban Hafsan Sojan Nijeriya Ya Sha Alwashin Inganta Tsaro A Yobe

by Muhammad Maitela and Sulaiman
5 months ago
in Labarai
0
Babban Hafsan Sojan Nijeriya Ya Sha Alwashin Inganta Tsaro A Yobe
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babban Hafsan Soja (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya sha alwashin shawo kan matsalar tsaro, inda ya ce za su yi dukkan abin yi wajen inganta tsaro, duk da wasu hare-haren da aka kai kwanan nan, a Buni-Gari da ke jihar.

Olufemi ya bayyana haka ne yayin ziyarar karfafa wa sojojin da ke bakin daga a jihar gwiwa a Yobe, inda ya kara da cewa, dangantakarsa da jihar ta musamman ce, wanda a baya ya kasance ya rike matsayin kwamandan Brigade da Sector 2 a jihar.

  • Ku Guji Rubuta Rahoton Farfagandar ‘Yan Ta’adda Mai Ɗaukar Hankali – Gwamnati Ga ‘Yan Jarida 
  • Tattalin Arzikin Sin Tamkar Teku Ne Ba Karamin Tabki Ba

“Mun zo ne a yau musamman don karfafa gwiwar al’ummar jihar Yobe da Sojojin mu da ke aikin samar da tsaro, duk da koma-bayan da muka samu, na sabbin hare-haren Boko Haram.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

“Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.”

Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da tura karin sojoji tare da kayan aikin tsaro.

Yobe

A nasa bangaren, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa COAS kan daukar matakan gaggawa wajen mayar da martani kan hare-haren kwanan nan, sannan ya yi wa sojojin da suka rasu addu’a.

Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji, inda ya bukaci karfafa hadin gwiwa wajen bayar da bayanan sirri don dakile matsalolin tsaro.

Gwamna Buni ya kara da cewa, “Dole mu hada kai mu yi aiki tare, tsakanin jami’an hukumomin tsaro wajen bayar da gudummawa tsakanin rundunonin tsaron Nijeriya.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

PSG Ta Yi Waje Rod Da Arsenal A Gasar Zakarun Turai 

Next Post

An Gano Cushen Biliyan 5 Cikin Kasafin Kuɗin Hukumar Alhazai Ta Ƙasa

Related

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta
Labarai

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

3 hours ago
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?
Manyan Labarai

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

6 hours ago
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

6 hours ago
Yobe
Labarai

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa

8 hours ago
An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki
Labarai

An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki

9 hours ago
Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi
Labarai

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

10 hours ago
Next Post
An Gano Cushen Biliyan 5 Cikin Kasafin Kuɗin Hukumar Alhazai Ta Ƙasa

An Gano Cushen Biliyan 5 Cikin Kasafin Kuɗin Hukumar Alhazai Ta Ƙasa

LABARAI MASU NASABA

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

September 19, 2025
Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

September 19, 2025
An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

September 19, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

September 19, 2025
Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

September 19, 2025
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

September 19, 2025
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

September 19, 2025
Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

September 19, 2025
Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

September 19, 2025
Yobe

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa

September 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.