Babban jami’in jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya yi kira da a yi nazari sosai tare da aiwatar da tunanin Xi Jinping kan al’adu.
Mamban zaunannen ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, kuma mamban sakatariyar kwamitin kolin JKS, Cai Qi ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da ya samu halartar jami’an yada labarai a fadin kasar, wanda aka gudanar a birnin Beijing daga ranar Juma’a zuwa Asabar.
Cai ya jaddada kokarin samar da tabbaci na akida mai inganci, da zaburarwa mai karfi, da kyakkyawan yanayin al’adu don gina kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni, da kuma ciyar da farfadowar al’ummar Sinawa gaba daga dukkan fannoni.
Cai ya kara jaddada sa kaimi ga inganta bunkasuwar yawon shakatawa da fadada mu’amalar al’adu da yin koyi da juna tsakanin al’ummomi. (Mohammed Yahaya)