Yanzu haka an shiga shekaru 10 na zagaye na 2 na karni na 21, kuma duniya na fuskantar kwaskwarima, da sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a tarihi, wanda ya zarce tunanin da ake yi.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana kwaskwarimar da ake fuskanta a matsayin “Babban sauyi da ba a taba ganin irinsa ba cikin karni daya”, wanda ya hada da kyautatuwar karfi tsakanin mabambantan kasashe da ya zarce zaton da aka yi a baya, matakin ya tabbatar da alkiblar da Sin za ta bi, har ma ya kunshi sauye-sauyen al’adu da wayewar kan Bil Adama.
Yau za mu ganin ma’anar maganar Xi Jinping kan wannan batu dake jawo hankalinmu.













