Kwanan baya, babbar darektar Hukumar Kiyaye Muhalli ta MDD ta UNEP Inger Andersen ta zanta da ‘yar jaridar Babban Rukunin Gidan Rediyo da Talabijin na kasar Sin wato CMG.
A yayin zantawarsu, ‘yar jaridar CMG ta bayyana cewa, a ranar 15 ga watan Agusta, an taya murnar ranar kiyaye muhallin halittu ta farko a kasar Sin. A wannan rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sake jaddada muhimmancin kare muhallin halittu a yayin da kasar Sin take kokarin neman dawamammen ci gaba.
Saan nan, Inger Andersen ta bayyana raayinta game da matakan da kasar Sin ta dauka wajen neman bunkasuwa ta hanyar kare muhallin halittu, kana, a yayin da ta ambaci raayin alummar kasar Sin na neman daidaituwa a tsakanin bil Adama da muhallin halittu, ta bayyana cewa, ta yi farin ciki sosai domin ganin an kafa ranar muhallin halittu a kasar Sin, wadda ta janyo hankulan jamaar kasa sosai. Wannan wata hanya ce da kasar Sin take bi domin neman dawamammen ci gaba, da kuma kiyaye duniyarmu. Haka kuma, ta kasance dabarar Sin wajen neman ci gaba cikin hadin gwiwa da kawar da talauci, kasar Sin ta kuma cimma burinta a wadannan fannoni ba tare da bata muhalli ba.
Ta ce, ranar kiyaye muhallin halittu ta kasar Sin da manufofin da kasar ta fidda su nuna cewa, muna da hanyoyi masu kyau wajen neman ci gaba, za mu samu daidaito a tsakanin zaman bil Adama da muhallin halittu, ya kamata mu dukufa wajen kare muhalli ta yadda dukkanmu za mu zama cikin wata duniya mai tsabta. (Maryam)