Babbar Kotun Tarayya mai lamba daya dake da zamanta a Jihar Kaduna Daura da ND, wacce mai Shari’a R.M. Aikawa, ke alkalanci, ta fara sauraran karar da wasu mahajjatan shekara ta 2024 su 64.
Mahajjatan sun dai maka Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ne tare da Hukumar Alhazain ta Jihar Kaduna a kan wasu hakkokinsu, da ba su cika musu ba a ya yin da suke gudanar da aikin hajjin na 2024.
- Hajji 2025: NAHCON Ta Tantance Kamfanonin Jiragen Da Za Su Yi Jigilar Alhazai Zuwa Saudiyya
- Kotu Ta Bayar Da Belin Yahaya Bello Kan Naira Miliyan 500
A hirarsa da manema labarai jim kadan bayan tashi daga zaman kotun, Barista Bashir Musa lauyan masu kara ya ce, “ Mun zo kotu ne, sakamakon mutanen da muke tsayawa a matsayin su na mahajjata da suka biya kudaden su na zuwa aikin hajji ta karkashin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna na shekarar 2024.”
Ya ce, wadanda muka tsayawa, sun rubuta wata takarda, suna bukatar sanin yadda aka yi kudadensu aka kashe su a lokacin aikin hajjin na 2024, ga su hukumar aikin hajji ta kasa da kuma ta Jihar Kaduna, wato suna bukatar wadannan hukumomin biyu, su bayani ta yaya aka yi da kudadensu da kuma yadda aka yi da Naira biliyan 90 wanda Gwamnatin Tarayya ta bayar a matsayin kudin tallafi na aikin hajjin na 2024, sakamakon yanayin yadda aka yi musu a Saudiyya, yadda aka karbe su a Saudiyya da yadda suka gabatar da aikin na su.”
Bashir ya ci gaba da cewa,“Wadnda muke tsayawar, akwai tambayoyi da suke da su akan yadda aka yi da wannan kudin, saboda ba a ba su kulawa yadda ya kamata ba a lokacin da suka kaddamar da aikin hajjin.”
Ya kara da cewa, da suka rubuta, har zuwa yau, an bayar da kwanuka 30 ga wadannan hukumomin, amma ba su iya bayar da wadannan bayanai a rubuce ba, shi ya sa muka garzaya zuwa kotu, domin kotun ta sanya su, na farko dai, muna son mu sani daga kotun shin ma muna da ‘yanci? To kotu ta sanya su tilas hukumomin su bayar da wadannan dalilan a kan yadda aka yi da wadannan kudaden a rubuce.
Ya sanar da cewa, wadanda suka shigar karar su 64 ne, domin wadannan bukatun, inda ya ce, iya sanin mu a cikin wadannan masu karar kowanne daya babu wanda ya biya kasa da Naira miliyan shida da dari shida da ‘yan kai na aikin hajjin na bana.
Bashir ya sanar da cewa, a zaman farko da kotun ta yi kan karar, amma Lauyan hukumar jin dadin Alhazai ta Jihar Kaduna suka aiko da takarda, suna bukatar a daga musu zuwa zaman kotun na gaba domin a yanzu suna gaban wata kotu, mu kuma ganin cewa wannan ne zama na farko sai muka ba su uzuri ba mu kalubalanci bukatar su ba, amma muna so su zo mu zauna, aji muhawarar ko wanne bangare.
A cewrsa, “ Fatanmu shi ne, su kawo dalilan da suka hana su duba wannan takarda da muka rubuta musu wanda kuma a karshe muna son kotu ta duba, idan wannan yanayin ya bukaci a sanya su su biya mu wasu kudade na wahalhalun da muka sha kotu ta sanya su su biya mu.
Kotun ta sanya ranar 21 na watan Janairu 2025 domin a dawo a saurari wannan sharia’ar.