Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa babban matsalar Nijeriya shi ne rashin shugabanci nagari. Ya ce dali’un wasu da ke ruke da madafun iko ne babbar matsalan Nijeriya bat sarin gudanarwa ba.
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban ma’aikatan hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja da suka yi wa ofishinsa kawanya domin nuna jin dadinsu da kuma godiya ga Shugaban kasa Bola Tinubu kan samar da hukumar kula da ma’aikata ta Babban Birnin Tarayya Abuja da sauran gyare-gyare.
- Saboda Kishin Ilimi Muka Raba Wa Makarantun Kano Littafai Sama Da Miliyan 2 – Kwamishinan Addini
- INEC Ta Tura Ma’aikata 46,084 Bayelsa, Imo Da Kogi Saboda Zaben Gwamnoni
Wike ya ce, “Mu ne matsalar kasar nan, mu masu rike da madafun iko, ba wai tsarin gudanarwa ba. Idan muka yarda da haka, karfin ikona zai ragu, kuma abin da kuka gani kenan duka. Babu wanda yake magana game da jin dadin wasu da kuma ci gabansu.
“Wane ne zai yi farin ciki a rayuwa idan ba zai iya kai wa kololuwar aikinsa ba? Idan ni alkali ne, zan so in kai har kotun koli. Idan ni ma’aikacin gwamnati ne, zan so in kai har matakin babban sakatare.
“Na tabbata cewa duk kun rasa kwarin gwiwa. Na gaya wa shugaban kasa cewa wannan lokaci ne na sake karfafa kwarin gwiwa. Wadannan ma’aikatan FCTA da suka rasa kwarin gwiwarsu yanzu su dawo da shi.
Ku fada musu cewa komai bai bace ba. Hanya daya tilo da za ku iya tabbatar musu da haka ita ce kai wa ga kololuwar mataki a wurin aikinku.
“Kuma mai girma shugaban kasa ya ce, bai san da haka ba. Yanzu da na sani, zan dawo da kwarin gwiwar ma’aikatan Babban Birnin Tarayya Abuja. Nan take ya amince da cewa mu aiwatar da dokar 2018, kamar yadda majalisar kasa ta zartar.
“Bari in gaya muku, daga yanzu zuwa mako mai zuwa zan aiwatar da shi, domin zan iya kai wa ga kololuwar mataki a cikin wannan mataki.
“Ya tabbatar da haka kuma ya yi mamakin abun da ya sa za mu zama cikas ga ci gaban wasu.”
Ministan ya ce zai mika godiyar ma’aikatan ga shugaban kasa.