Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tura jimillar ma’aikatan 46,084 saboda zaben gwamna da za a gudanar a jihohin.
Zaben gwamnoni zai gudana ne a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihohin Bayelsa, Imo, da Kogi.
- Farashin Kayan Abinci Ya Karu Da Kashi 26.72
- Rikicin Gaza: Ana Ci Gaba Da Tir Da Kisan Fararen Hula A Harin Asibiti
Sai dai hukumar ta nuna damuwa game da rashin tsaro da tashe-tashen hankula masu alaka da zaben.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja, inda ya kuma bayyana cewa hukumar ta kuma amince da masu sa ido 11,000 a zaben.
Ya ce: “Kamar yadda muka sha fada, mun damu da rashin tsaro da tashe-tashen hankula da suka shafi zabe a jihohin uku.
“Haka zalika, hukumar za ta gudanar da jerin taruka da masu ruwa da tsaki a matakin kasa baya ga ci gaba da gudanar da ayyukan a matakin jiha.”
“Ya zuwa yanzu mun amince da kungiyoyi 126 na kasa da kasa tare da tura masu sa ido 11,000 don zaben.”
Tuni ya bukaci jami’an tsaro su yi aiki tukuru don tabbatar da tsaro sannan ya yi alkawarin gudanar da sahihin zabe a jihohin uku.