Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yuni, 2023 a matsayin ranakun hutu don gudanar da bikin Sallah Babba ta bana.
Wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Oluwatoyin Akinlade, ya bayyana a ranar Litinin a Abuja.
Sanarwar ta bukaci Jama’a da su gudanar da shagulgulan biki lafiya.
Gwamnatin ta taya al’ummar musulmi a Nijeriya da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje murna bisa zagayowar Idin Layya tana mai cewar, “Muna fatan al’ummar musulmi za su yi addu’o’i a lokutan bukukuwan ga ci gaban zaman lafiyar kasa da bunkasarta mai daurewa.” In ji sanarwar.