Shahararren dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Dan asalin kasar Croatia Luka Modric.Â
Ya rattaba hannu akan karin shekara daya a Madrid da zai barshi a kungiyar har zuwa 2024.
- An Dakatar Da Mourinho Wasanni 4 Kan Fada Da Alkalin Wasa
- Ronaldo Ya Kafa Tarihin Zama Ɗan Wasan Da Ya Fi Kowa Buga Wasannin Ƙasa Da Ƙasa
Modric mai shekaru 37 wanda ya bugawa Real Madrid wasanni 488 ya lashe kofunan Laliga 3 tare da Uefa Champions League 5 tun bayan zuwansa Madrid daga Tottenham.
Talla
Ya zama tsoffin yan wasa uku kenan da suka kara kwantiragi a Madrid da suka hada da Nacho Fernandes da Toni Kroos.
Real Madrid ta dauko matashin dan wasan Ingila Jude Bellingham daga Borrusia Dortmund da zata hada da wadanda take dasu domin tunkarar kakar wasa ta badi.
Talla