Masarautar Katsina ta sanar da soke hawa a bikin shagugulan Babbar Sallah na ranar Asabar mai zuwa.
Sakataren Majalisar Masarautar, Alhaji Sule Mamman-Dee, ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar a jihar, inda sanarwar ta ce, masarautar ta dauki wannan matakin ne saboda yanayin lamarin rashin tsaro a jihar.
- Hajin Bana: Saudiyya Ta Kara Wa Maniyyatan Nijeriya Wa’adi
- Yanzu-yanzu: Abba Kyari Bai Bace Daga Gidan Yari Kuje Ba, Cewar Hukuma
Sanarwar ta kara da cewa, Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir-Usman, ya nuna damuwarsa matuka kan lamarin rashin tsaro a yanzu a wasu sassa na masarautar, inda sanarwar ta ce, Sarkin zai kawai halarci Sallar Idi a ranar Asabar.
Bikin hawan sallah a bisa ala’adar masarautar an shafe shekaru ba a gudanar ba, wanda mahaya dawakai ke nuna basirarsu iri-iri ta wajen wasa da dawakan.