MADAM ADESUWA OGECHI UDO, matashiya ce wadda ta tashi cikin maraici da rashin gata, amma hakan bai hana ta samun yin karatu har zuwa matakin Jami’a ba. Sannan ta yi gwagwarmaya a bangarori iri daban-daban, wanda ya kai tag a zama shahararriyar ‘yar fim na Hausa da kuma Turanci. Bugu da kari kuma, a halin yanzu ita ce Shugabar Gidauniyar ‘Empowerment Foundation (ELS)’, wacce har Masallaci ta gina tare da tallafawa marasa galihu ba tare da nuna banbancin addini ko kabila ba, duk kuwa da kasancewar ta na kirista wadda ba musulma ba. Ta samu kyatuka da lambar yabo a kashashen Turai kamar Ingila da Amurka da kuma nan gida Nijeriya. Wakilinmu MUSTPHA IBRAHIM KANO, ya samu zantawa da ita kamar haka:
Za mu so mu jin cikakken sunanki da takaitaccen tarihinki a takaice?
Sunana ADESUWA OGECHI UDO, an haife ni a Kano amma iyayena mutanen Jihar Benin ne, na yi makarantar Firamare a kwakwaci daga nan na wuce Sakandire ta Danware duk a nan Kano, daga nan kuma sai na tafi Jami’ar Jos, inda na karanta ilmin fannin sana’ar wasan kwaikwayo (Film), bayan kammala Digirin nawa sai na kama hanya Legas, inda na fara fitowa a fina-finan Turanci (Nigerian Film). Daga nan ne kuma sai likkafa ta ci gaba, domi akalla na yi fina-finai dai-dai har guda 25, na Hausa kuma sun kai 11. Kazalika, daga cikin Fina-finan da na yi akwai; Lafiya uwarjiki, Musa Bakanike da sauran makamantan su, cikin wadanda na fara shirin wasan Hausa da su a matsayinsu na jarumai akwai Baba Ari, Ali Nuhu, Hannatu Bashir da sauran su.
Wane suna aka fi sanin ki da shi a Fina-finanki?
Madam ELS, wanda kuma shi ne sunan Gidauniyarta (ELS Empowerment Foundation), wadda ke samar da ayyuka da tallafawa Marayu raunana da sauran marasa galihu a fannoni daban-daban.
Me ya jawo hankalinki kika kafa wannan Gidauniya?
To, magana t gaskiya ita ce na ta so cikin matsala ta rayuwa, domin kuwa sai da na yi tallan ruwan sanyi da ake daurawa a leda, na kwandala kwandala, sai na sayar sannan ni da Kakata za mu samu mu ci abinci, duk sanda aka ce ruwan babu sanyi haka zan yi ta faman kuka, idan na koma gida Kakar tawa sai ta rarrashe ni da ce da ni ka da ki damu Allah zai ba mu abin da za mu ci. Sannan a hakan idan ta yi abinci, sai ta diba ta rararraba wa wadanda ba su da shi, haka nan idan ta yi miya da nama, shi ma sai ta rarraba wa mabukata. Kazalika, tallan ruwan nan haka nake dauka tun daga cikin Sabon gari wajen titin Sarkin yaki har zuwa ‘Yan kura da sauran wasu gurare daban-daban a kasa. Da haka dai cikin ikon Allah aka rayu har aka yi makaranta.
Ko za mu iya sanin tsakanin Marayu da sauran Raunana nawa wannan Gidauniya taki ta tallafawa?
Babbar magana! Gaskiya abin kamar da wuya, dalili kuwa zai yi wuya na san adadin mutanan da suka amfana da wannan Gidauniya, amma dai kiyasin da na yi zi iya kai wa kinanin dubu dari biyu (200,000), domin mu kan fita mu yi sansani, mu tattara mutane masu rauni wasu mu koya musu sana’o’i mu kuma ba su jari, musamman mata iyayen Marayu da sauran su. Mun yi wannan a wasu Unguwanni na Birnin Kano, kamar
Unguwar Sabon gari, Birget, Unguwa Uku da sauran makamantan su tare da raba musu kayan sana’o’i. Ko a shekarar da ta gabata, mun yi irin wannan sansani a Gidan Makama da ke kusa da Fadar Kano, cikin Karamar Hukumar Birni da kewaye, ta hanyar tara daruruwan mata muka koya musu sana’o’i iri daban-daban, muka kuma ba su jari da atamfofi da kayan abinci, baya ga daukar nauyin abincinsu na kwana bakwai, akwai kuma lokacin horar da su sana’o’in kamar yadda na fada maka a baya.
Har ila yau, bayan Kano wannan Gidauniya ta ta je har wasu jihohin don taimaka wa raunanan. Akwai jihata ta asali Jihar Benin, sai Bayalsa, Ibadan da kuma Jihar Kaduna, duk wannan Gidauniya ta je ta yi aikin bayar da tallafi da kuma koya sana’o’i da bayar da jari ko kayan sana’a da suka hada da; Injin kitso (drier), Injin Markade da sauran makamantan su, domin mata su samu abin dogaro da kawunansu.
Ko akwai wasu ayyuka da wannan Gidauniya ta yi tun bayan kafuwarta?
Kamar wasu watanni da suka shude ina Kasar Ingila, na ba da umarnin a gina masallaci a nan cikin Sabon gari, domin amfanin al’ummar musulmi wadanda muke tare da su, sannan na nemi alfarmar mai Martaba Sarkin Kano, a zo a bude shi. Wannan masallaci yana nan a cikin Sabon gari, titin Sarkin yaki, sai kuma rumfuna guda takwas da na samar domin anfanin leburori wadanda ke zama a ciki kafun su samu aiki ko bayan sun dawo daga kwadagonsu, musamman saboda maganin rana ko lokacin damuna ko kuma shan iska duk karkashin wannan Gidauniya.
Haka zalika, akwai kuma tsarin gangami da nake jagoranta na shiga Unguwar Sabon gari tare da hadin guiwar masu ruwa da tsaki, domin wayar da kawuna da kuma yakar al’adar nan ta sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma sace-sace, musamman na wayoyi da karuwanci da sauran makamantan su.
A irin wannan gangami da muke fita ne na ci karo da wani abin takaici da kuma ban tausayi, inda na hadu da wata mata mai shekara 68 tana karuwanci. Na ce da ita ke ya haka? ta ce da ni yanzu haka ma duka aka yi mata; aka kuma dauke kayanta ciki har da wayarta, bayyan an yi lalata da ita na tsawon awanni 24, aka kuma hana ta kudinta duk kuwa da cewa a kullum tana baiwa Otal din da take kwana Naira 1000. A nan ne bayyana min cewa, da zarar ta samu jari za ta koma jiharsu ta
Akwa Ibom ta kama sana’a.
Kafin kammala wannan tattaunawa da ke Ogechi a sana’arki Ta Fim me ya fi faranta miki rai?
Gaskiya abubuwan da suke faranta min rai suna da yawa, amma dai wannan tallafi da Uban giji ya ba ni dama nake yi ya fi faranta min rai. Sa’annan kuma kyatukan yabo da na samu a Kasashen Ingila da Amurka
da kuma nan gida Nijeriya, musamman Kano ba karamin abin alfahari ne a wurina ba. Kamar a shekarar 2022, na samu kyauta a matsayin mace wacce ta fi taimako a Afirka baki-daya (The Best Women Philanthropy Award) sai kuma kyautar lambar yabo a bangaren Fim ita ma da na samu a Ingila ta (ZAFA ZAFA Award) da kuma wata kyautar daga ‘ICAN’ da sauran kungiyoyi daban daban a Nijeriya da kuma wajenta. Wannan dalili yasa mu ma muka baiwa Ubanmu, uban kuma wannan Gidauniya mai Martaba Sarkin Alhaji Aminu Ado bayero, kyautar girmamawa ta ‘ELS’ dangane da gudunmawa da hadin kan da muke samu daga wurin sa.
Mene ne ba za ki iya mantawa da shi a rayuwarki ba?
Abubuwan da ba zan manta da su ba suna da yawa, amma abin da ya fi damuna nake jin badadi koda-yaushe shi ne, lokacin da ba ni da halin taimakawa, sai wata mata wadda mijinta ya mutu ya bar ta da ‘ya’ya biyar, ‘yan’uwan mijin nata suka kwashe dukiyarsa suka kama gabansu. Ko shakka babu, wannan mata ta shiga matukar tashin hankali. A daidai wannan lokaci ta zo wurina na taimaka mata, ba ni da halin d azan taimaka mata, ga shi yanzu kuma ban san a inda zan same ta ba. Don haka, duk lokacin da na tuna wannan yana ba ni tausayi da kuma takaici. Sai kuma wani tsoho da ya zo guna ya ce shi ma na taimaka masa da Naira 1,500, na ce da shi Baba mai za ka yi da shi? ya ce zai je ya yi cefane ne gidansa saboda babu abin da za a ci, sannan ya zo neman aikinsa na gyaran fanfo; bai samu ba.
Me kika fi so ko kauna a rayuwarki?
Abin da na fi so da kauna a rayuwata shi ne, ganin na taimaka wa Marayu da raunana marasa galihu suna cikin farin ciki tare da jindadi. Idan kuma t akama na shiga cikin su muna rawa, muna nishadi da murna, kai wannan yana faranta min rai kwarai da gaske a rayuwata.
A karshe wane sako kiki da shi ga gwamnatoci da sauran al’umma?
Sakona a nan shi ne, Shugaban Kasa, Gwamnonin Nijeriya da Shugabanin Kananan Hukumomi da sauran Shugabannin Addini, su dubi halin da al’umma suke ciki na matsin rayuwa, su taimaka musu ta
hanyar koya musu sana’o’i tare da ba su jari da kuma tallafin kayan Abinci, musamman ga raunana da sauran Marayu. Haka nan, su ma mawadata su yi kokarin tallafa wa marasa shi da sauran mabukata. A takaice wannan shi ne kadai abin da zance iya cewa.