Da yake tofa albarkacin bakinsa, shugaban kamfanin dillalan mai a Nijeriya (IPMAN), Abubakar Maigandi ya bukaci ‘yan Nijeriya da cewa ka da su tayar da hankulansu dangane da bayanin basuka da yawan kudin jigila, musamman kan harsashen karuwar farashin litar mai.
“Babu wani bukatar ‘yan Nijeriya su firgita kan batun kalubalen kudi da NNPCL ke ciki. Ba bakon abu ba ne a basuka a lamarin kasuwanci. Muna aiki tare da Typical wajen ganin an ci gaba da samar da mai ba tare da yankewa ba ga ‘yan Nijeriya.
- Za A Ci Gaba Da Fuskantar Karancin Man Fetur – IPMAN
- Tallafin Man Da Nijeriya Ke Biya Yanzu Ya Zarce Nb700 Duk Wata – IPMAN
“Idan akwai karin farashin litar mai, NNPCL za ta sanar, haka nan da wadatar samar da mai din dukka,” ya shaida.
Da aka tambayeshi kan nawa ‘yan kasuwa ke sayar da litar mai sai ya ce, “Wadanda suka samu mai ta hannun NNPCL da ke sayarwa kan naira 650 zuwa 700 a lita guda, wadanda suke samu kuma daga hannun masu zaman kansu suna sayarwa ne a kan naira 920.”
Ya kuma ce wadanda suke daukowa daga Legas zuwa kamar Maiduguri da wasu wurare farashin litarsu na zarce naira 920.
A Jihar Nasarawa, Neja da kuma Kogi ana sayar da litar mai ne a tsakanin naira 850 zuwa naira 1,100 daga ranar Litinin da ta gabata yayin da ‘yan jarida suka yi zagayen duba halin da ake ciki.
A jihohin Delta, Bayelsa, Kurus Ribas, Imo, Inugu da kuma Abiyaa mazauna sun tabbatar da cewa su ma suna sayen litar mai ne daga kan kudi naira 870 zuwa 1,000.
Shi kuma manajan kamfanin BBH Consulting, Barr. Ameh Madaki, ya shaida cewa gwamnatin Tinubu ta kasa iya tafiyar da harkokin mai yadda ya dace. Ya bukaci gwamnatin da ta tashi tsaye ta hanzarta daukan matakan da suka dace wajen shawo kan kalubalen da suka dabaibaye lamarin mai kafin lamarin ya fi karfinta.
Ya ce, muddin gwamnati ta bari farashin mai ya kara tashi a wannan lokaci, hakan ya nuna akwai sakaci da rashin damuwa da halin da ‘yan Nijeriya ke ciki.