Yayinda ake ci gaba da buga wasannin share fage na shiga gasar cin kofin nahiyar Afirika. Hukumar kwallon kafa ta Afirika (CAF), ta fitar da sunayen alkalan wasan da za suyi alkalanci a gasar ba tare sunan dan Nijeriya ko guda daya ba.
Ana kallon Nijeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashen da suka fi shahara a harkar kwallon kafa a nahiyar.
Alkalan wasan da suka fi yawa a cikin jerin sunayen sun fito ne daga kasashe biyu na arewacin Afirka, wato Masar da Aljeriya.
Hukumar CAF ta sanya sunayen alkalan wasa 85 daga sassa daban-daban, gabanin gasar cin kofin Afirka na shekarar 2024 da kasar Cote d’Ivoir zata karbi bakunci.
A gasar da aka fafata wadda Kamaru ta karbi bakunci a baya, Samuel Pwadutakam, shi ne dan Nijeriya daya tilo da aka saka cikin alkalan wasa 63 a gasar AFCON da ta gabata kuma shima yaje ne a matsayin mai jiran ko ta kwana.