Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Misis Zainab Ahmed ta kara jaddada cewa babu gudu ba ja da baya sai gwamnatin tarayya ta cire tallafin mai a watan Yunin 2023.
Zainab ta ce tuni an ma fara shirye-shiryen cire lallafin man mai dogon zango da zai fara aiki tun daga 2023 har 2025.
Ministar ta bayyana hakan ne lokacin da take jawabi wajen rufe taron tattalin arziki karo na 28, inda ta siffanta tallafin mai da hatsarin da ya turnike tattalin arzikin Nijeriya, wanda babu makawa sai an cire shi.
Ta yaba wa shawarar Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Mista Shubham Chaudhuri wanda ya fadakar da cewa tallafin babban illa ne ga tattalin arzikin Nijeriya.
Da yake tattaunawa da ministar, Chaudhuri ya ce cire tallafin zai kawo samun lafiyar harkokin kudade a kasar nan. Ya ce cire tallafin zai samar da karin kudaden shiga ga gwamnatin tarayya wajen cike gibin karacin kudade.
Daraktan bankin duniya ya kara da cewa a yanzu haka kasar tana bukatar gudanar da matakan na gaggawa, domin dakatar da hanyoyin da kudade suke sulalewa. Ya ce Nijeriya tana bukatar kara kashe kudade wajen abubuwan da suka kamata, domin samun karin kudaden shiga da kuma kashe kudaden ta hanyar da suka kamata a lokacin da ‘yan kasa suke biyan haraji.
A halin yanzu dai, gwamnatin tarayya ta tabbar wa jihohi cewa za su samu raran kudade wadanda suka hada da biliyan 1 wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ta kange ta hanyar cike gibin canjin naira karkashin shirin bankin duniya na harkokin kudade.