Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso ya ce babu gudu babu ja da baya a yaki da hauhawar farashin kayayyaki.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron kwamitin tsare-tsarena kudi a Abuja, Cardoso ya ce bankin zai ci gaba da tura duk wasu kayan aikin da ake da su don magance hauhawar farashin kayayyaki.
- Man Fetur Da Ake Shigowa Ya Ragu Da Kashi 35 – CBN
- CBN Ya Bayyana Shirin Kakaba Wa Bankuna Takunkumi
“Bari in fara cewa babban bankin ya jajirce wajen ci gaba da yaki da hauhawar farashin kayayyaki. Babu ja da baya kan hakan.
“Za mu sanya komai a cikin makamanmu don tabbatar da cewa mun sami damar inganta shi, kuma ba shakka, wannan ya hada da komawa ga manufofin kudi wanda aka saba da shi.
“Don haka, ina ganin yana da muhimmanci a bayyana hakan a gaba, babu gudu babu ja da baya kan hakan, ”in ji Cardoso
Cardoso ya ce tasirin manufofin kudi na daukar lokaci don samar da sakamako, tare da jinkirin watanni shida zuwa tara, ko ma har zuwa shekara guda, ya danganta da matakan da aka aiwatar.
Gwamnan CBN ya yi hasashen cewa tasirin tsauraran manufofin na baya-bayan nan zai kara fitowa fili nan da kwata na farko na shekarar 2025.
“Muna sa ran ganin sakamako mafi girma a cikin kwata na farko na 2025, kuma za ku iya yin lissafin tun lokacin da muka fara karfafawa, don haka muna sa ran ganin wannan a farkon kwata na 2025,” in ji shi.
Cardoso ya kuma ce babban bankin yana aiki tare da hukumomin da abin ya shafa don magance kalubalen tsarin da ke shafar hauhawar farashin kayayyaki, kamar tabarbarewar wadatar kayayyaki da na matsalolin kayayyakin more rayuwa.
Ya kara da cewa CBN yana kuma kokarin ganin an kawar da gurbatattun da ake samu a kasuwar canji domin tabbatar da cewa ya fito da hakikanin darajar naira.