Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa duk yadda wani zai faɗa maka matsalar kan sha’anin tsaro bai kai wanda abin ya shafa kai-tsaye ba.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin jawabinsa a taro kan sha’anin tsaro da gwamnonin Arewa maso Yamma da hukumar UNDP suka shirya a Katsina.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 9 Da Sace 50 A Jihar Katsina
- Atiku Ya Ziyarci Buhari Da Sarkin Daura Da Kuma Sarkin Katsina
Haka kuma gwamnan ya bayyana abin da ya banbanta taron da suka je ƙasar Amurka da kuma wanda suke gudanarwa a halin yanzu a Katsina.
Tun daga can Amurka muka yanke hukuncin cewa mu dawo gida mu shirya irin wannan taro domin duk abin da wani zai fada maka bai kai wanda abin ya same shi ba’ inji Radda.
Gwamna Radda ya ce haƙiƙa manyan bakin da suka halarci wannan taro sun nuna kwarewa da nuna kishi wanda hakan zai iya zama izina domin tunkarar matsalar baƙi ɗaya.
Ya ƙara da cewa a ƙarshen wannan taron na kwana biyu da ake yi, za a ƙaru da shawarwarin masana wanda za su ɗora a kan shawarwarin da aka ba su da kuma abubuwan da suke yi.