Tsohon Dan Majalisar Tarayya na Kananan Hukumomin Kiru da Bebeji, Abdulmuminu Jibril Kofa, ya ce a matakin da ake babu wani dan siyasa da zai fice daga jam’iyyar NNPP da zai girgiza siyasar Kwankwaso.
Yayin wata hira da gidan talabijin na Channels, Kofa, ya bayyana zamansa mai magana da yawun yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP.
- Da Dumi-Dumi: ‘Yansanda Sun Cafke Wani Dan Bindiga Dan Shekara 20 A Kaduna
- Za Mu Sa Kafar Wando Daya Da Masu Fasa Bututun Mai
A kan batun sauyin sheka da ake tunanin Sanata Ibrahim Shekarau zai yi daga NNPP zuwa wata jam’iyyar, Kofa ya ce ko Sanatan ya sauya sheka, jam’iyyarsu za ta kai labari a 2023.
Kofa, ya ce a 2019 an ga aya a zaben Kano, inda duk manyan ‘yan siyasa suka tare a APC, amma Rabiu Kwankwaso ya nuna musu nauyinsa, don haka babu wani wanda zai iya kada NNPP, domin Kwankwaso ya rike siyasar Kano, a cewarsa.
“A 2019 abun takaici, dukkaninmu sai mu ka bi Ganduje, Shekarau, Kabiru Gaya, Barau Jibrin, Kawu Sumaila, duk wani babba a Kano ya bi Ganduje, Me ya faru? Kwankwaso shi kadai a gefe guda, ya doke mu a zaben gwamna. Abin da ya faru a zaben, abin da aka gani ne, amma a gaskiya ya ci zabe.
“Saboda haka idan ana zawarcin Shekarau, me ake nema ne, na gagara fahimtar wannan. Babu wanda zai bar NNPP a Kano da zai jijjiga Kwankwaso.”
Kamar yadda gidan rediyon Nasara da ke Kano ya wallafa, ya ce, Kofa wanda ya wakilci Kiru da Bebeji a majalisar tarayya ya ce hakan bai nufin yana kokarin cin mutuncin tsohon gwamna Shekarau, illa martani ga rade-radin da ake yi na cewa Malam Shekarau na neman barin NNPP, yayin da wasu ke zargin ya sa labule da sauran ‘yan takarar 2023.
A makon da ya gabata ne dai rahotanni suka karade kafafen watsa labarai cewa Shekarau zai fice daga NNPP sakamakon gaza cika masa wasu alkawura, abin da Kwankwaso ya ce sam ba haka bane, kuma babu wata matsala a tsakaninsu.