Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya soki wadanda suka sauya sheka zuwa APC a yankin arewa maso yamma, inda ya danganta su da son rai maimakon jin dadin al’umma.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa na PDP na shiyyar arewa maso yamma a Kaduna ranar Asabar.
- Kotu Ta Daure Hadimin Tambuwal Kan Yada Bidiyon Da Ake Wa Matar Gwamna Liki Da Dala
- Za Mu Tabbatar Majalisa Ta Yi Watsi Da Dokar Haraji – Sanata Tambuwal
“Mutane suna canza jam’iyyarsu saboda dalilai daban-daban, amma abin da na lura shi ne, wadannan sauye-sauyen ba su shafi bukatun jama’a ba, sun shafi ci gaban kansu ne,” in ji shi.
Ya kuma yi Allah wadai da gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC, inda ya zarge ta da rashin hangen nesa, tausayi, da alkibla.
A cewarsa, duk wani dan siyasa mai hankali ba zai yi tunanin komawa jam’iyyar APC ba, idan aka yi la’akari da matsalar tattalin arziki da ake fama da ita da kuma gazawar gwamnatin Tinubu.
Tambuwal ya bukaci ‘yan adawa da su hada kai su tsara dabarun tunkarar zaben 2027, yana mai jaddada bukatar bai wa ‘yan Nijeriya mafita mai inganci.
“Babu wani abin burgewa a APC wanda ya wuce amfanin kashin kai. Mu da muke kokarin saka kishin kasar nan wajen yi wa kasa hidima na gaskiya mu hada kai don korar wannan gwamnatin a 2027, domin ta gaza share wa ‘yan Nijeriya hawayensu.”
A halin da ake ciki kuma, jam’iyyar PDP a yankin arewa maso yamma ta sake jaddada aniyarta ta kwato mulki a shekarar 2027, inda ta jaddada muhimmancin hadin kai a tsakin ‘ya’yan jam’iyyar.
Sanarwar da aka fitar a karshen taron, wanda shugaban jam’iyyar PDP na yankin arewa maso yamma, Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya karanta, ya kara jaddada aniyar jam’iyyar na dawo da shugabancin Nijeriya.