Hukumomin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sun yi watsi da rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani masallaci a yankin, inda suka kashe wani limami da wasu masallata.
Wata kafar yada labarai ta yanar gizo mai suna ‘Sahara Reporters’ ce ta yi zargin cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan wani masallaci a Sabon Birni, sun kashe limamin, sun kum harbe wasu masallata sannan suka sace wasu.
- Rikicin Boko Haram Ya Daɗe Fiye da Yaƙin Basasar Najeriya – Obasanjo
- Kwamitin Kolin JKS Ya Saurari Shawarwarin Jami’an Da Ba ‘Yan Jam’iyyar Ba Game Da Ayyukan Raya Tattalin Arziki
Amma da yake magana da jaridar ‘Daily Trust’ a ranar Asabar, Shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Ayuba Hashimu, ya bayyana rahoton a matsayin karya wanda bai faru ba.
“Ban san wani masallaci da aka kai wa hari ba, balle batun kisan limamin da masallatan. Labarin karya ne,” in ji shi.
A nasa ɓangaren, ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar, Aminu Boza, ya ce babu wani lamari makamancin haka da ya faru a yankin.
“Ban san yadda suka sami labarinsu ba, amma ba gaskiya ba ne. Babu wani masallaci da ‘yan bindiga suka kai hari,” in ji shi.
Hukumomin tsaro a jihar har yanzu ba su fitar da rahoton wani hari makamancin haka ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.














