ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Boko Haram Ya Daɗe Fiye da Yaƙin Basasar Najeriya – Obasanjo

by Abubakar Sulaiman
9 months ago
Obasanjo

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa yaki da ’yan Boko Haram a Nijeriya ya wuce tsawon Yaƙin Basasa na 1967–1970. Obasanjo ya yi wannan tsokaci ne ranar Lahadi a shirin Toyin Falola Interviews, wanda aka watsa kai tsaye a kafafen sada zumunta, inda Bishop Matthew Kukah da tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Moghalu suka halarta.

Ya ce dakile ‘yan ta’adda na bukatar haɗin dabaru na musamman, da kayan aiki na zamani, da bayanai masu inganci, da fasahar zamani. Obasanjo ya ce babu laifi sojojin Nijeriya su samu horo daga ƙasashen da suka yi nasara wajen yaki da ‘yan ta’adda, inda ya kawo Colombia a matsayin misali. Ya jaddada cewa horon sojoji na yau da kullum ba ya isa wajen tunkarar ‘yan ta’adda da suke yawo ko shiga cikin jama’a.

  • Obasanjo Ya Buƙaci Matasa Su Karɓi Ragamar Shugabanci A Ƙasashen Afrika
  • Kuskure Ne Tattaunawa Da Ƴan Bindiga, Yafi Dacewa A Nemi Tallafin Ƙasashen Waje – Obasanjo

Obasanjo yayi gargadin cewa rashin kyakkyawar hanyar siyan kayan yaki da musayar bayanai zai iya kawo koma baya a yaki da ‘yan ta’adda, yana mai cewa bai kamata a bar sojoji su kadai su sayi kayan yaki ba, domin harkar ta zama kamar masana’antu. Daga kwarewarsa wajen yaki da masu tada zaune tsaye a Niger Delta, ya bayyana cewa ba za a iya kawar da yiwuwar haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’adda ba.

ADVERTISEMENT

Tsohon shugaban ya ce: “Sai da yaƙin basasa ya ɗauki watanni 30, duk da cewa mun yi tsammanin zai ɗauki watanni shida. Amma wannan yaki da ‘yan ta’adda da masu laifi ya ɗauki kusan shekaru 15.” Obasanjo ya kara da cewa ya ziyarci Maiduguri a 2011 domin fahimtar asali, da koke-koke da tsarin shugabancin Boko Haram. Ya kuma bayyana cewa a farko ‘yan ta’addan sun ƙi tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, kafin daga bisani su amince da tsagaita wuta na kwanaki 21, wanda bai yi tasiri ba saboda rashin kyakkyawar tattaunawa da shugabanninsu

Obasanjo
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Bukola Saraki Ya Je Bauchi Ta’aziyyar Ɗahiru Bauchi

Bukola Saraki Ya Je Bauchi Ta'aziyyar Ɗahiru Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.