Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a yayin taron manema labarai na yau da kullum Talatar nan cewa, babu wani takunkumi da zai iya toshe ci gaban kimiyya da fasaha na kasar Sin.
Wani dan jarida ya gabatar da tambaya cewa, sau da dama wasu kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka, sun yi ikirari tare da neman hana ruwa guda, kana wasu kasashen ketare sun nuna damuwa cewa, za a dakile ci gaban kimiyya da fasaha na kasar Sin, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Mao Ning ta yi karin haske kan wannan batu.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp