A ranar Alhamis ce Tsohon Shugaban Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari zai gurfana a gaban kotun duniya (ICC) a Birnin Paris bisa zarginsa da hannu wajen badakalar kwangilar aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla.
Wani kamfanin samar da wutar lantarki mai suna ‘Sunrise Power’, ya shigar da karar gwamnatin tarayya kan Dalar Amurka biliyan 2.3 bisa zargin cewa Nijeriya ta gaza cika alkawurran da ta kulla da kamfanin.
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Babu Wanda Zai Ci Nasara A Yakin Cinikayya Ko Yakin Harajin Kwastam
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
Wata majiya mai tushe da ta zanta da LEADERSHIP, ta tabbatar da faruwar lamarin. “Eh, tsohon shugaban kasar zai ba da bayanai ranar Alhamis a Faransa kan lamarin,” in ji majiyar.
Lamarin dai ya shafi ikirarin da kamfanin Sunrise Power ya yi dangane da yarjejeniyar gina tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla mai karfin megawatt 3,050 a jihar Taraba a shekarar 2003, wanda darajarsa ta kai Dala biliyan 6.
Kamfanin dai ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawurran kwangilar da ta rataya a wuyanta, wanda ya kai ga yin shari’a a kotun ICC.
A halin da ake ciki kuma, fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin kafafen sada zumunta na baya-bayan nan da ke nuni da cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya tursasa manyan ‘yan Nijeriya da su shiga tsakani.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, mai ba Shugaban Kasa Shawara a Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana ikirarin a matsayin “Karya da yaudara.”
“Tsarin sasantawa ya kasance sirri ne, kuma wadanda ke da hannu a cikin tsaron Nijeriya suna yin haka ne bisa radin kansu, saboda kishin kasa da kuma jin dadin aiki,” in ji Onanuga. “Babu inda shugaba Tinubu ya matsa wa wani ya shaida ko kuma ya hana kowa yin hakan.”
Wani kamfanin wutar lantarki mai suna Sunrise Power, ya fara gudanar da shari’ar a ranar 10 ga Oktoba, 2017, inda ya nemi diyyar Dala biliyan 2.354 kan abin da ya bayyana a matsayin karya yarjejeniyar kwangila.
Kamfanin ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta karya yarjejeniyar 2003 na aikin Mambilla, wanda aka kirkira da farko a matsayin tsarin “gina, aiki, da canja wuri”
A shekarar 2017, ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje na lokacin Babatunde Fashola ya bayyana Sunrise Power a matsayin “mai tsaka-tsaki,” inda ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta dauki kamfanin Sinohydro Corporation Limited, wani kamfani na kasar China, a matsayin dan kwangilar aikin Injiniya, saye da gine-gine (EPC). .
Sai dai yayin da aka ce an amince da yarjejeniyar ta Dala miliyan 200 a shekarar 2020, daga baya Sunrise Power ta shigar da sabuwar kara kan Dala miliyan 400 a kotun ICC, tana mai zargin gwamnati da kin cika sharudan sasantawa. Har ila yau, kamfanin ya nemi a maido da shi a matsayin abokin hulda na aikin Mambilla na Dala biliyan 5.8 da aka sakewa fasali, a cewarsa an cire shi a tattaunawar da ta biyo baya.
Wakilin Lauyoyin Sunrise, Femi Falana ne ya shigar da karar a kotun ta ICC, inda ya bukaci gwamnati ta biya diyyar Dala miliyan 400 da kuma tarar da ta saba wa yarjejeniyar. Bukatar hakan ta kunshi hukuncin ba da kashi 10 cikin 100 na jinkiri fiye da kayyadaddun lokutan sasantawa na kwanaki 14 da aka amince da su a cikin Janairu 2020.
Gwamnatin tarayya ta bayar da hujjar cewa an sake duba sharudan yarjejeniyar ne saboda matsalar kudi da annobar Korona ta haifar, wanda ya haifar da sabuwar tattaunawa.
Sakamakon sulhun na iya yin tasiri sosai ga harkokin kudi na Nijeriya da kuma makomar aikin wutar lantarki na Mambilla da aka dade ana jan kafa.
A halin yanzu dai Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo yana Birnin Paris don karrama goron gayyatar da aka yi masa na yin jawabi kan aikin samar da wutar lantarkin Mambila.
LEADERSHIP ta nakalto cewa tsohon shugaban ya bar Nijeriya zuwa Birnin Paris a safiyar ranar Asabar domin samun damar bayyana ya kuma yi magana a kan lamarin, wanda zai iya ci gaba da tafiya kamar yadda muke magana.
Mataimaki na musamman ga Obasanjo kan harkokin yada labarai, Kehinde Akin Yemi, ya tabbatar wa LEADERSHIP a ranar Litinin da yamma a Abeokuta cewa Obasanjo ya zabi girmama gayyatar ne domin daidaita al’amura.