Wasu jiga-jigan ‘yan siyasa daga jam’iyyun NNPP da ADP a Jihar Kano, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.
Sauya sheƙar na zuwa ne yayin wani taro da da ya gudana a gidan Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, a Abuja.
- Kare-Karen Haraji Ba Zai Bunkasa Arzikin Amurka Ba
- NLC Ta Yi Zanga-Zanga A Ofishin Wike, Ta Nemi A Biya Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi Albashin N70,000
Shugaban APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas, na cikin waÉ—anda suka halarci taron.
Daga cikin waɗanda suka suya sheƙar zuwa APC akwai Sanata Kawu Sumaila, Hon. Kabiru Alhassan Rurum wanda ke wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure a Majalisar Tarayya, da Hon. Abdullahi Sani Rogo wanda ke wakiltar Karaye da Rogo.
Har ila yau, akwai Hon. Zubairu Hamza Massu wanda ɗan majalisa ne a Majalisar Dokoki ta Jihar Kano mai wakiltar Sumaila wanda shi ma ya sauya sheƙar.
Tsoffin kwamishinoni na Jihar Kano kamar su Hon. Diggol, Hon. Abbas Sani da Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Baffa Bichi su ma sun koma APC.
Hakazalika, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar ADP a zaɓen 2023, ya sauya sheƙa zuwa APC.
Ana kallon wannan sauya sheƙar a matsayin wani babban tagomashi ga jam’iyyar APC musamman a Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp