Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, CON, ya amince da gudanar da gasar karatun Alkur’ani na shekara ta 2022 a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sanya hannun mukaddashin sakataren hukumar ilimin Arabiyya da addinin musulunci ta jihar Kebbi, Alhaji Hassan Haruna wanda kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi
Sanarwar ta ce, an shirya gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki tsakanin ranakun 4 zuwa 7 ga watan Disamba, 2022, inda aka shirya gudanar da bikin rufe gasar a ranar Alhamis 8 ga watan Disamba, 2022 a dakin taro na masaukin shugaban kasa da ke Birnin Kebbi.
Gasar ta jahar ita ce matakin karshe na shirye-shiryen halartar tawagar jihar don halartar gasar karatun Alkur’ani ta kasa karo na 37 da za a fara a jihar Zamfara daga ranar 16 zuwa 24 ga watan Disamba, 2022.
Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Danfodio Sokoto ce ta shirya taron na kasa.
Mukaddashin sakataren hukumar, Alhaji Hassan Haruna ya yabawa Bagudu bisa tallafin da ya bayar don samun nasarar shirin da kuma ayyukan hukumar.