Gwamna Atiku Bagudu, na Jihar Kebbi, ya amince da fitar da Naira miliyan 30 ga tawagar ‘yan wasan jihar da ke halartar gasar wasannin motsa jiki ta kasa na ‘yan wasa da jami’ai 115 da ke halartar bukukuwa 10 a bikin da aka yi daga ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba a garin Asaba ta Jihar Delta.
Naira miliyan 30 ne dai za a yi amfani da su wajen jigilarsu, likitoci, kayan aiki da alawus-alawus.
- Za A Gudanar Da Taron Tunawa Da Jiang Zemin A Ranar Talata Mai Zuwa
- Ko Da Gaske Ne Kasar Sin Barazana Ce?
Har ila yau, gwamnan ya saki Naira miliyan 50 domin siyan riga da kwallaye ga kungiyoyin kwallon kafa a kananan hukumomi 21 da ke jihar.
Za a yi amfani da kudin ne wajen siyan riguna guda 50 ga matasan ’yan kwallon kafa saiti 50 na manya, manya-manya 260 na kungiyoyi guda 260, da rigunan wando guda 200 da kuma kwallaye 2,500.
Abubakar Dakingari, Babban Sakataren Yada Labarai na gwamnan,ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a Birnin Kebbi da aka raba wa manema labarai, inda ya ce an dauki matakin ne don inganta harkokin wasanni a jihar.
Ya kara da cewa an fitar da Naira miliyan uku domin tallafa wa masu shirya gasar kwallon kafa ta Gwamnonin Nijeriya, wanda za a gudanar a Birnin Kebbi.