Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wani kudirin doka da za ta ci tarar naira N25, 000 ga duk wanda aka samu ya yi fitsari, bahaya, zubar da shara ko kuma zubar da majina a kan titi ko kuma a ƙarkashin gada a jihar.
Hakan ya biyo bayan dokar da majalisar ta zartar wanda zai bai wa hukumar da ke ƙawata birane damar kula da wuraren shakatawa.
- Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe
- Sin: Kasar Amurka Ce Ta Haifar Da Matsalar Miyagun Kwayoyi A Cikin Gidanta
A zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar na yau Litinin, shugaban ma su rinjaye na majalisar, ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala, Lawal Hussaini Dala, ya ce hakan ya zama dole domin bai wa gwamnati cikakken goyon bayan da take buƙata wajen tsaftace jihar Kano domin ganin ta yi kafada-da-kafada da manyan birane a duniya a fannin tsafta da ci gaba.
Lawal Hussaini ya kara da cewa, kari a kan tarar naira dubu 25, akwai hukunce-hukunce da dama a ƙarƙashin dokar ga duk wanda aka kama ya karya dokar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp