Shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin ya gargadi jami’an shari’a a fadin kasar cewa dole ne a tabbatar da adalci ga kowa – Talaka da mai kudi, ba tare da nuna wata wariya ba, ko karɓar cin hanci, “bai dace adalci ya zama na sayarwa ba.”
Da yake jawabi a yayin bude taron alkalan Nijeriya na kotunan koli na shekarar 2025 a Abuja, Tinubu ya jaddada cewa jami’an shari’a su ne ainihin masu kula da adalci, don haka, shugaban ya tabbatar da goyon bayansa kan samar da walwala, horo, da inganta Cibiyar Shari’a ta Kasa.
Ya ce, “bai dace adalci ya zama na sayarwa ba, kuma Majalisar Shari’a bai dace ta zama mafaka ga masu aikata laifuka ba.
- Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC
- Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi
“Cin hanci da rashawa a kowane ɓangaren gwamnati, zai raunana ɓangaren ne kawai, amma cin hanci da rashawa a ɓangaren Shari’a zai ruguza ɓangaren ne gaba ɗaya.”
Don haka, dole ne a tabbatar da gaskiya da adalci, yana mai jaddada cewa kare mutuncin kotunan alhakin kowane jami’in shari’a ne, ba wai Majalisar Shari’a ta Kasa kawai ba.
ADVERTISEMENT













