A wannan makon da muke ciki, za a gudanar da wasannin kusa da na karshe, na gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya dake gudana a Qatar. Da fatan kafofin yada labarai za su mai da hankali kan gasar ita kanta kadai.
Qatar ita ce kasa ta farko cikin kasashen Larabawa da ta karbi bakuncin wannan kasaitacciyar gasa a duniya. Amma tun lokacin da ta fara neman iznin daukar bakuncin gasar, kasashen yamma suka rika takalar ta, suna cewa wai wasu ma’aikatan ginin filayen gasar fiye da dubu 10 sun mutu, da nufin zuga wutar da za ta sa sauran sassa su bayyana kin yardarsu a fannin diplomasiya, har an ce, kasashen yamma suna siyasantar da gasar ta wannan karo.
Matsalar ta wannan karo, ba ta shafi Qatar kadai ba a tarihin wasan motsa jiki na duniya.
Domin kuwa, a gasar Olympic ta lokacin hunturu ta Sochi, da ta Beijing, har ma da gasar FIFA ta Qatar ta wannan karo, kafofin yada labarai na kasashen yamma, sun dauki mataki iri daya, na shafawa kasashen bakin fenti, ta fakewa da wasu batutuwa. Dalili shi ne bambancin ra’ayi da suke ta nunawa kasashe da ba na yammaci ba, da ma nuna wariyar launin fata. (Amina Xu)