Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau cewa, ya kamata Amurka ta dakatar da yin amfani da ma’auni biyu kan batun kare hakkin dan Adam, da kuma siyasantar da batun jin kai na zirin Gaza.
Wang Wenbin ya bayyana haka ne lokacin da yake tsokaci game da sanarwar Amurka ta watan Ramadan a jiya, inda sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya ce musulmai ‘yan kabilar Uygur ta jihar Xinjiang ta kasar Sin, da ‘yan kabilar Rohingya na kasar Myanmar da kasar Bangladesh, da Palesdinawa na zirin Gaza, suna fama da rikice-rikice tare da fuskantar mawuyacin hali.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, ana samun zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arziki da zaman jituwa a tsakanin mabiya addinai a yankin Xinjiang na kasar Sin, kuma ana tabbatar da hakkin dan Adam na daukacin jama’a, ciki har da ‘yan kabilar Uygur. Ya ce yankin Xinjiang na kasar Sin ba ya fuskantar rikici, amma zirin Gaza na fuskantar rikice-rikice. Haka kuma musulmai na yankin Xinjiang ba sa fama da yunwa ko kora ko kisa, amma miliyoyin musulmai na zirin Gaza suna fama da wadannan matsaloli. (Zainab Zhang)