Kocin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Mauricio Pochettino ya bayyana cewar ya kamata Chelsea ta samu wani matsayi a gasar Firimiya zuwa yanzu, amma ba ta tsaya a matsayi na 10 ba.
Pochettino ya bayyana haka ne ga manema labarai jim kadan bayan tashi daga wasan da kungiyarsa ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da ci 2-1 a Old Trafford.
- Manchester City Tayi Rashin Nasara A Hannun Aston Villa Da Ci 1-0
- An Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa A Zamfara Bisa Kashe Abokinsa Akan N100
Pochettino ya kara da cewar ‘yan wasan Chelsea na bukatar kara nuna kwazo da jajircewa domin ganin sun dawo da martabar kungiyar a idon Duniya.
Talla
Daga karshe Pochettino ya yi fatan dawowar ‘yan wasan kungiyar dake jinya cikin lokaci domin ci gaba da taka leda.
Talla