An nuna damuwa game da basussukan da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ta ciyo, rashin aikin yi ga matasa, da cewa bai kamata sabuwar gwamnati mai zuwa ta bi sahunta ba.
Shugaban mujami’ar majalisar ‘yan uwa a Nijeriya (EYN), Rabaran Joel Billi, ya bayyana haka a taron fastoci da wakilan mujami’ar karo na 76, da ya gudana a hedikwatar cocin da ke Kwarhi a karamar hukumar Hong a jihar Adamawa.
- Mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Modibbo Adama Ya Rasu
- NNPP Ba Ta Da Kudin Kalubalantar Nasarar Tinubu A Kotu –Buba Galadima
Ya ci gaba da cewa “Wannan bashin ba zai kyale sabuwar gwamnati mai zuwa ta iya samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar kasar nan ko aikin yi ga matasa ba.
“Da kamar wuya gwamnati mai zuwa ta iya biyan basusukan da ake bin Nijeriya kuma ta samu zarafin gudanar da ayyukan ci gaban kasa.
“Ina kira ga gwamnati mai shigowa da ta zama mai sauraren jama’a, ta rika bibiya da jin koke-koken mutane, ba kamar yadda gwamnatin shugaba Buhari ta yi kememe kan batun El-Zakzaky,” ya jaddada.
Da yake magana game da taron fastocin cocin da ya gudana a ranar Alhamis, shugaban cocin ya ce “taronmu ya cimma nasarori, muna fatan fastoci da wakilai, za su yi amfani da irin koyarwar da su ka samu, hadi kan al’ummar Nijeriya shi zai tabbatar da kasarmu ta zauna lafiya a matsayin abu daya” in ji Billi.
A karin bayanin da ya yi wa manema labarai, babban sakataren gudanarwar mujami’ar na kasa, Rabaran Dakta Daniel Mbaya, ya ce taron ke da alhakin zartar da kodurorin da cocin za ta aiwatar a shekarar nan da ma shekara mai zuwa.
Ya ce mahalarta taron sun fito ne daga jihohin kasar nan, da wasu kasashen duniya, inda ya ce manufar taron shi ne samar da ingantaccen zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista da ma wadanda ba su da kowane Addini.