Babban sakatare a hukumar kula da jin dadin Alhazai na Jihar Filato, Barista Auwalu Abdullahi ya bayyana cewa bai wa hukumomin kula da alhazai na jihohi ‘yancin gashin kai zai taimaka wajen inganta aikin hajji a kasar nan.
Ya ce sami tsawon shekaru biyu ba a sami zuwa aikin hajji ba, amma a bana ya jagoranci mahajjatan jihar zuwa kasar Saudiyya don aikin hajjin wannan shekara ta 2022, bayan kasar Saudiyya ta dage dokar haramci da ta gindaya wa kasashen Musulmi na zuwa kasar domin gudanar da aikin hajji sakamakon cutar Korona.
- Mauludi: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar 10 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Hutu
- Jakadan Kasar Sin Ya Bayyana Damuwa Kan Yadda Ake Nuna Bambanci Ga ‘Yan Kananan Kabilu Yayin Da Ake Aiwatar Da Doka A Wasu Kasashe
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa d awakilimmu da ke Jos, bisa yadda aikin hajjin bana ya gudana bayan dage dokar.
A cewarsa, kowanne aikin hajji yana da irin nasa kalubale, sai dai an sami gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali da lumana.
Yace tuni kasar Saudiyyar ta bai wa kasashen musulmai umurnin fara gudanar da shirin aikin hajjin shekarar 2023 kuma hukumar jin dadin alhazai ta kasa ta kira taro na tattaunwa a game da matsalar da ake samu na rashin jigilar wadansu mahajjata da kamfanonin jiragen saman da aka ba su aikin kwasan alhajai, don a sami a mayar musu da kudadensu, wadanda suke da niyyar tafiya a shekara mai zuwa kuwa, sai a sake yin masu rajista.