A jiya Laraba ne aka bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na 8, bikin na wannan karo wanda zai gudana har zuwa ranar 10 ga wata, ya hallara kasashe, da yankuna, da kungiyoyin kasa da kasa har 155. Kazalika, kamfanoni 290 dake cikin jerin kamfanoni 500 dake kan gaba a duk fadin duniya sun halarci wannan gagarumin baje koli. Lamarin da ya bayyana niyyar kasar Sin ta neman bude kofa, da habaka hadin gwiwa tare da cimma moriyar juna.
Wane irin tabbaci bikin CIIE karo na 8 ya samar ga kasashen duniya?
Da farko dai akwai tabbatar da bude kofa ga waje. A shekarar 2024, ma’aunin bude kofa na kasar Sin ya karu da kaso 0.5 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2023. Kana, a tsakanin shekarar 1990 zuwa shekarar 2024, ma’aunin bude kofa na kasar Sin ya karu da kaso 29.6 bisa dari, adadin da ya kai kan gaba a duk fadin duniya.
A sa’i daya kuma, kamfanonin kasashen ketare sun samu tabbacin bunkasar kasar Sin ta hanyar halartar bikin na CIIE. Wasu shugabannin kamfanonin kasashen ketare sun bayyana cewa, kasar Sin na da manyan kasuwanni masu bude kofa, da yanayin zuba jari mai dacewa, tare da manufofi masu karko, wadanda suke janyo hankulansu matuka.
Haka zalika kuma, a matsayin dandalin shigowa da kayayyaki na musamman a duniya, bikin CIIE ya samar da tabbacin cimma moriyar juna ga kasashen duniya. A bana, a karon farko, an kafa dandalolin nune-nunen kayayyaki daga kasashe mafiya fama da talauci, tare da fadada yankunan nune-nunen kayayyakin kasashen Afirka. A halin yanzu, akwai kamfanoni har 163 daga kasashe mafiya fama da talauci da suka halarci baje kolin na CIIE, adadin da ya karu da kaso 23.5 bisa dari, idan aka kwatanta da na bara. Kana, yawan kamfanoni daga kasashen Afirka ya karu da kaso 80 bisa dari a wannan karo. (Mai Fassara: Maryam Yang)














