Baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE a takaice da yake gudana a karo na 6 a birnin Shanghai, ya samu yabo daga jagororin kasashen duniya, da jami’ai daga sassa da dama, wadanda suka jinjinawa gudummawarsa a matsayin dandali dake samar da tarin damammaki ga ’yan kasuwa, da kamfanonin duniya baki daya.
Kaza lika sun yaba da yadda baje kolin ke taka rawar gani, wajen yaukaka hadin gwiwar cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa, tare da ingiza hadin gwiwar tattalin arziki da ci gaban duniya gaba daya.
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Farko Na Shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” Kan Musayar Kimiyya Da Fasaha
- An Bude Bikin CIIE A Shanghai
Game da hakan, mataimakin shugaban kasar Afirka ta kudu Paul Mashatile, ya jinjinawa kasar Sin bisa yadda take kara bude kofofin kasuwanninta ga duniya, musamman ma ga kasashen Afirka. A cewarsa, baje kolin CIIE ya samarwa kamfanonin duniya wata dama ta baje hajoji da hidimominsu, tare da zarafin fadada cudanya da abokan hulda.
A nata tsokaci kuwa, babbar sakatariyar taron MDD game da cinikayya da samar da ci gaba Rebeca Grynspan, cewa ta yi CIIE ya shaida kudurin kasar Sin na daidaita alakar cinikayya da sauran sassan duniya.
Grynspan ta kara da cewa, baya ga kawar da shingen cinikayya ko karfafa zuba jari, kasar Sin ta kuma shaidawa duniya aniyarta ta gabatarwa duniya sabbin dabarun samar da ci gaba da musayar al’adu. (Saminu Alhassan)