Shugaban kungiyar masu harkokin kasuwanci ta na’urorin zamani ta Sin da Turai dake Brussels, Luigi Gambardella ya ce bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin CIIE, gayyata ce ga kasashen duniya su ci gajiyar damarmakin kasuwar kasar Sin tare da hada hannu tare domin samun moriyar juna.
A cewar Luigi Gambardella, CIIE alama ce bayyananniya cewa, kasar Sin na mara baya ga dunkulewar tattalin arzikin duniya, kuma a shirye take ta bude kofar kasuwarta ga duniya.
- Ruto: Aikin Hadin Gwiwa Karkashin Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ya Kawo Babban Canji Ga Kenya
- Ministan Wajen Sin Ya Yi Kira Da A Tsagaita Wuta A Gaza
A cewarsa, baje kolin CIIE na da muhimmin tasiri kan tattalin arziki, kuma zai bayar da gudunmuwa ga habaka harkokin cinikayya na kasar Sin da bunkasa cinikayya a duniya, a lokacin da ake matukar bukatarta.
Ya kuma yaba da yadda aka samar da wani dandalin hadaka na musammam, ta hanyar tattara shugabannin kasuwanci da jami’an gwamnatoci da masana sana’o’i daga fadin duniya a wuri guda. Yana mai cewa, irin wannan hadaka za ta iya haifar da sabbin damarmakin kasuwanci da hadin gwiwa.
Har ila yau, Gambardella yana ganin bikin na CIIE a matsayin dandalin kaddamar da sabbin kirkire-kirkire, kamar sabbin mutum-mutumin inji da ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi kamar na lantarki da sabbin nasarorin da aka samu a fannin kirkirarriyar basira ta AI. Yana mai cewa, wadannan fasahohi za su bunkasa sana’o’i tare da shawo kan kalubalen duniya. (Fa’iza Mustapha)