Babban malamin addinin Islama a Kaduna jihar Dakta Ahmed Mahmoud Gumi, ya bukaci daukacin musulmin Nijeriya da su fito da murya daya su yi Allah wadai da abin da yake faruwa a kasar Fasdinu.
Dakta Gumi, ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a yau Juma’a yayin taron manema labarai da Jakadar kasar Fasaldinu a Nijeriya Abdallah Abu Shawesh, wanda ya gudana a dakin taro na masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kara Karbo Bashin Dala Biliyan 3.45 Daga Bankin Duniya
- Shin Wasan Kwaikwayon Na Zaben Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Ta Kawo Karshe Ne?Â
Dakta Gumi, ya ce “Bamu yarda da mulkin wariya ba a kasar Fasaldinu kuma ya zama duk wani dan Nijeriya ya fito ya nuna rashin amincewasa a murya daya saboda yadda ake kashe yara kanana da rusa wurin ibada tare da yanke musu wuta da ruwan sha da kuma kashe ‘yan jarida a Gaza”
Akan haka ya bukaci gwamnatocin Nijeriya da ta tallafa wa Fasadinawa kamar yadda sauran kasashe suke yi wanda zai nuna cewa ita ma ta damu da abin da yake faruwa a kasar.
“Kamar yadda gwamnatin kasar indiya ta bayar da tallafin kudi dala miliyan 30 ga Falasdinawa muna kira ga gwamnatin Nijeriya ta yi koyi da irin matakin gwamnatin kasar indiya” in ji shi.