Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi watsi da rahotannin da ke cewa ya fice daga jam’iyyar PDP.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 ya jaddada cewa, yana gangamin tarayya ne da sauran jam’iyyun siyasa domin tunkarar kayar da jam’iyyar APC a 2027.
- Shugabannin Larabawa Sun Amince Da Tsarin Gina Gaza Da Zai Lakume Dala Biliyan 53
- Da A Ce Ni Ba Dan Fim Ba Ne, Da Na Zama Malamin Addinin Musulunci -Baba Rabe
A kwanakin baya dai rahotanni daban-daban sun nuna cewa Atiku na tunanin barin jam’iyyar PDP a shirye-shiryen tunkarar zaben shugaban kasa na 2027.
Rahotanni sun bayyana cewa, ya kammala yunkurin komawa jam’iyyar SDP.
Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ofishin yada labarai na Atiku ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya na nan dan jam’iyyar PDP na gaskiya.
Yayin da yake bayyana rahotannin a matsayin “karya”, ofishin yada labaran ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton sauya jam’iyyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp