Yau shekaru 55 da suka gabata, an kashe Martin Luther King, wani mai rajin kare hakkin dan adam, kana dan asalin Afrika a Amurka, a birnin Memphis dake jihar Tennessee, wanda ya girgiza duk fadin duniya.
Bayan shekaru 55, a cikin wannan birni, ’yan sandan Amurka 5 sun bugi wani ba’amurke dan asalin Afirka mai shekaru 29 a duniya, Tyre Nichols har ya mutu, wanda ya fusata dukkan al’ummar Amurka.
Daga daren ranar 27 zuwa ranar 28, ga watan, zanga-zanga ta barke a cikin gomman biranen Amurka. Kafofin watsa labarai na kasar na fargabar rikicin da “mutuwar George Floyd” ya haddasa a duk fadin Amurka a shekarar 2020, zai maimaita kansa.
A zahiri, dalilin da ya sa Amurkawa ’yan asalin Afirka su kan fuskanci abubuwa irin wannan daga ’yan sandan Amurka shi ne, ra’ayin nuna kabilanci dake karkashin tsarin dimokuradiyyar Amurka.
Bisa alkaluman da shafin intanet na Mapping Police Violence, mai bibiyar ayyukan cin zarafi da ’yan sandan Amurka ke yi ya fitar, a cikin shekarar 2022, ’yan sandan Amurka sun kashe mutane 1186, cikinsu Amurkawa ’yan asalin Afrika, sun kai kashi 26 cikin dari, amma jimillar Amrukawa ’yan asalin Afirka ita ce kaso 13 cikin dari kawai bisa na al’ummun Amurka.
Ban da wannan, hukumar binciken yaduwar kananan makamai a Switzerland ta yi hasashen cewa, yawan bidigogi da mutane suke rike da su a Amurka ya kai miliyan 393. Wato yawan bindigogi sun fi yawan mutanen kasar, wanda a hakika dai, ba ma kawai ya sa ’yan sandan Amurka fuskantar yanayin hadari ba, har ma ya sa sun fi son daukar matakan nuna karfin tuwo a lokacin da suke sauke nauyin dake bisa wuyansu. Sakamakon haka, wannan mummunan abu ya kasance kamar wani “ciwon Amurka” da ya yi ta tsananta a kai a kai. (Safiyah Ma)