Shugaban hukumar kwallon kafar Afirika (CAF) Patrice Motsepe a karon farko ya yi magana game da yanayin da tawagar kwallon kafar Nijeriya ta tsinci kan ta a Libya bayan zuwa buga wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON).
Patrice Motsepe ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai inda ya yi Allah wadai da halin da Super Eagles ta Nijeriya ta shiga a filin tashi da saukar jiragen sama na Libya gabanin wasan neman gurbin shiga gasar AFCON 2025, Motsepe ya yi Allah wadai da lamarin amma ya dage cewa ba zai yi magana kan lamarin ba har sai hukumar ta yanke shawara ta karshe.
“Ya kamata mu kasance masu hakuri a kowane lokaci amma dai yanzu ba zan ce komai ba har sai lokacin da hukumar CAF ta kammala cikakken bincike akan abinda ya faru in ji shi,amma ina so in jaddada cewa wannan wani abu ne da ba za mu lamunta ba, kuma za a dauki matakin da ya dace.
Na ji labarai da dama a kan abubuwan da suke faruwa a lokacin da wata kasa ta ziyarci wata kasar domin buga kwallo a nan Afirika, har ma na ji wani lokaci ana neman su bayar da takardun shaidarsu ta zama ‘yan kasa, sannan a lokacin cutar Korona sai a dubi mutum 10 da suka fi kwarewa a wasa ace suna dauke da cutar Korona da sauran korafe korafe wadanda ba za mu yarda hakan ta ci gaba da faruwa ba.
Ya ci gaba da cewa a tunanina dukkan wadannan abubuwan su na faruwa sakamakon rashin daukar wani mataki a kan masu aikata hakan,to ku sani cewa zamu gabatar da wasu tsauraran dokoki da za su taimaka wajen gyara harkar kwallon kafa a nahiyar Afirika in ji Motsepe.
Tun da farko dai an shirya Nijeriya za ta kara da Libya a wasan zagaye na biyu a Talatar makon jiya ranar 15 ga watan Oktoba, 2024, amma hakan bai yiwu ba sakamakon janyewa daga wasan da Nijeriya ta yi bayan shafe awanni 20 a filin jirgi ba tare da samun kulawa daga hukumomin kasar Libya ba.