Dan wasan tawagar Argentina Lionel Messi ya ce, ya yanke shawarar komawa kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami, saboda ba ya samun farin ciki lokacin da yake buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Paris St-Germain.
Messi mai shekara 37, ya lashe Ligue 1 karo biyu da French Cup a 2022 a kaka biyu da ya yi a PSG, daga baya ya bar kungiyar a shekarar 2023.
- ‘Yansanda A Legas Sun Kama Mutum 35 Da Ake Zargi Da Fashi Cikin Mako Guda
- Gwamna Dauda Ya Rantsar Da Shugaban Ma’aikatan Zamfara Da Sakatarori 12
”Sa hannu da na yi da Inter Miami dama ce, saboda wasu abubuwan da suka faru a baya a Paris Saint German, kuma hukunci ne da ya kamata na dauka, saboda na bar Barcelona, sannan na yi kaka biyu ba tare da ina jin dadi ba, ba na farin ciki kwana biyu a jere tun daga wajen atisaye da buga gasa, na kasa sabawa da abubuwa da yawa,” in ji Messi, mai Ballon d’Or takwas a hirar da ya yi da Apple Music Messi, wanda ya lashe La Liga 10 da Champions League hudu da Club World Cup uku a Barcelona ya bar kungiyar a shekarar 2021. Hakan ya biyo bayan da Barcelona ba za ta iya biyan dawainiyar Messi ba, wanda ya kara rattaba kwantiragin ci gaba da buga wasa a kungiyar na tsawon kakar wasa biyu.
Dalilin da ya sa ya zama wajibi Messi ya koma Paris St Geramin kan yarjejeniyar kaka biyu.
Bayan da Messi ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin duniya a Katar a 2022, sai magoya bayan PSG suka juwa masa baya, sakamakon rashin kokarin kungiyar a Champions League.
Haka kuma an dakatar da shi, saboda zuwa Saudi Arabia ba tare da izinin mahukuntan PSG ba da ta kai bai samu halartar atisaye ba. Dan wasan tawagar Argentina, wanda ya koma Inter Miami, bayan ta yi mai tsoka daga manyan kungiyoyi ya ce ya koma Amurka ne domin ya taimakawa gasar kasar ta kara bunkasa a duniya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp