Shugaban cocin Living Faith ta Nijeriya, Bishop David Oyedepo, ya ce bai taba ganin cin hanci da rashawa mafi muni ba a tarihi tunda aka kirkiri kasar Nijeriya ba sama da na gwamnantin APC Mai mulki a karkashin Gwamnatin shugaba Buhari.
Bishop ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taro da aka gudanar a cocin, inda ya koka kan halin kuncin da kasar ta fada, wanda ya alakanta da cin hanci da rashawa da ya ta’azzara a mulkin.
Ya ce almundahanar da ake zargin dakataccen Akanta Janar da ita kawai ta isa ta warware matsalolin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) da ke gudanar da yajin aiki a yanzu haka. Rahoton Aminiya
Ya kuma ce, “Yara da dama na barin karatu saboda rashin kudin da za a biya makaranta, daliban jami’ar ma da tallafi daga al’umma suke iya karasa karatun.”
Ya kuma bayyana cewa, “Gwamnatin Buhari ta gaza wajen ikirarinta na yaki da cin hanci da rashawa, kuma babu yadda za a yi a shafe wannan acikin tarihin Nijeriya da ya afku a karkashin jagorancin shi (Buhari).”