A ranar Asabar din da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), a Jihar Edo, ta bayyana cewa daga cikin katin zabe na dindindin 30,979 (PVC) da suke ajiye ana jiran masu karba a jihar, ya zuwa yanzu 1,348 ne kawai aka karba.
Jami’in hukumar mai kula da wayar da kan masu kada kuri’a, Timidi Wariowei ne ya bayyana hakan a karshen mako a Benin yayin da yake zantawa da manema labarai kan ci gaba da rijistar masu kada kuri’a a jihar.
Wariowei ya ce, “Tun daga watan Janairun 2022, muna da jimilar Katin Zabe na Dindindin 30,979 muna jiran masu karba. Amma daga cikin wadannan adadi, Kati 1,348 ne kawai masu su suka karba.”
Ya koka da cewa rashin karbar ba ya karfafa musu gwiwa, don haka ya yi kira ga jama’a da su zo su karbi katin zaben su domin kada kuri’a a zaben 2023 mai zuwa.
Wariowei ya kuma bayyana cewa, a ci gaba da yin rijistar masu kada kuri’a da ake ci gaba da yi, hukumar ta yi wa kimanin mutane 69,448 rajista a jihar.