Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewar bayan ya rasu bai amince ba kuma bai yarda a ware rana ta musamman a ranar 2 ga watan Al-Muharram domin ake yin Mauludin tunawa da ranar haihuwarsa ba.
Marigayin ya bayyana haka ne daga cikin wasiyyar da bayar, cikin tawali’u da ƙanƙan da kai ya ce shi bai kai wanda za a ke gudanar da Maulidin tunawa da shi ba kamar yadda ake yi wa Manzon Rahama, irin su Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim Inyass.
- Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 25 A Wani Sabon Hari Kan Iyakar Kano
- Gwamnatin Kano Ta Musanta Jita-jitar Barazanar Tsaro A Jihar
Marigayi wanda ya rasu a ranar Alhamis ya bayyana cewar shi kawai Muƙaddami ne daga cikin Muƙaddaman Shehu, kuma hadiminsa sannan surukinsa inda ya bayyana cewa hakan ma kawai ya ishe sa alfahari.
Shehu Dahiru Bauchi ya nuna cewa, idan har an ce kowani Muƙaddamin Shehu za a ke masa Maulidin tunawa da shi to kowani rana ma zai zama na gudanar da maulidodi ne domin yawan Muƙaddaman da ake da su.
Ya bayyana da bakinsa cewa: “Amma ni ban yarda a ce wata rana za a yi taro, yau 2 ga watan Muharram ranar da aka haifi Shehu Dahiru, ita muke yi wa Maulidi, ban yarda ba, kada a yi min bayan rasuwa ta.
“Amma na ji wani yana cewa, Rabi’ul Auwal ya kunso mana (ya zo mana) da Annabi Muhammadu (SAW), Safar ya kunso mana Shehu Tijjani (RA), Rajab ya kunso mana Shehu Ibrahim (RA), ya ce wai Muharram ya kunso musu Shehu Dahiru to wannan kada a sake fada, kada na sake ji.
“Ni ba kowa ba ne cikin wannan tsarin, ni Muƙaddami ne. Ni Muƙaddami ne daga cikin muƙaddaman Shehu. Yanzu kowani Muƙaddamin Shehu sai an masa Maulidi ranar haihuwarsa nawa kenan? akwai ranar da za ta wuce ba a samu Maulidi ba?
“In an ce kowani Muƙaddamin Shehu za a masa Maulidi akwai ranar da ba Maulidi ke nan a Nijeriya? To ban yarda kada a sa sunana a cikin waɗanda ake ma wannan abu,” in ji shi.
Ya sake fayyace wasiyyar tasa da cewa, “Kuma ko na mutu kada a ce yau ranar biyu ga watan Muharram za a yi Maulidin Shehu Dahiru, ban yarda ba!, ban yarda ba!!; A bar ni kamar sauran ‘yan uwana Mukaddamai.”
Ya sake nanata cewa shi “Ni ba kowa ba ne illa muƙaddami cikin Muƙaddaman Shehu kuma wannan ya isheni alfahari, hadiminsa kuma surukinsa, Alhamdulillahi.”
A gefe guda ya ce Maulidin tunawa da Shehu Ibrahim da ake yi a watan Rajab shi ne ya fara gudanarwa.














