Tsohon Shugaban ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai na Arewacin Nineriya (Arewa Film Makers
Association of Nigeria, AFMAN) na ƙasa, kuma jarumi a Masana’antar Kannywood, Alhaji Abdullahi Sani (Baba Karami), ya nuna ɓacin ransa kan wani hoto da ake yadawa a kafafen sada zumunta, inda ake nuna shi a kan keken marasa kafafu cikin wani yanayi na tsananin rashin lafiya, kuma aka rubuta cewa; ya yi nadamar shiga harkar fim.
Baba Karami, ya shaida wa mujallar fim cewa; wannan maganar sam babu ƙamshin gaskiya a cikinta, domin kuwa babu wani ko wata da na yi maganar danasanin shiga harkar fim da shi ko da ita, haka zalika babu wata kafar yada labarai da na yi hira da ita, kuma na fada musu wannan magana in ji shi, kawai dai wasu ne suka ƙirƙiri labarin, don biyan buƙatun ƙashin kansu.
Ya kara da cewa, wannan hoto da ake yadawa; an dauke shi ne a wani shirin fim da na fito, mai taken ‘Aliyah’, don haka, ba hoto na ba ne na zahirin yadda nake, hoton fim ne.
- Muradun ‘Yan Nijeriya A 2023 Kan Siyasa, Tsaro Da Tattalin Arziki
- Bai Kamata Mutum Ya Dogara Da Harkar Fim Kadai Ba -Hamza Talle Mai Fata
A game da batun lafiyarsa kuwa, Baba Karami cewa ya yi, “Na yi rashin lafiya a kwanakin baya, har na kwanta a asibiti; sakamakon ciwon hawan jini da nake fama da shi, amma dai a yanzu na samu sauƙi ƙwarai da gaske, ina kuma ci gaba da gudanar da harkokina da nake yi.
ɗon hakaa cewar tasa, waccan magana da ake yadawa; ƙarya ce, sannan kuma duk wanda yake yada wannan magana, babu makawa miƙiyi na ne, ina mai bai wa masoyana haƙuri sakamakon yadda hankalinsu ya tashi da ganin labarin, ni dan fim ne, kuma ina ci gaba da ayyukan da nake yi na fim, ban kuma yi nadama ko danasanin harkar fim da nake yi ba, in ji Baba Ƙarami.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp