ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bangare Japan Da Ya Dage Sai Ya Zubar Da Dagwalon Ruwan Nukiliya Cikin Teku Zai Sha Kunya Ta Tsawon Tarihi

by CMG Hausa
2 years ago
The Joban Joint Power Co. Nakoso thermal power station, rear, in Iwaki, Fukushima Prefecture, Japan, on Tuesday, July 4, 2023. Japanese utility Tepco is planning to release more than 1 million cubic meters of treated radioactive water — enough to fill 500 Olympic-size swimming pools — from the wrecked Fukushima Dai-Ichi nuclear power plant into the Pacific Ocean, part of its nearly $150 billion effort to clean up the worst atomic accident since Chernobyl. Photographer: Soichiro Koriyama/Bloomberg

A ranar 7 ga wata, Hukumar Kula da Makamshin Nukiliya ta Japan, ta ba da takardar shaidar amincewa da na’urorin zubar da dagwalon ruwan nukiliya na Fukushima, ga Kamfanin Wutar Lantarki na Tokyo. Hakan na nufin gwamnatin Japan ta kara daukar wani mataki na shirin zubar da dagwalon ruwan nukiliyar cikin teku, duk da tsananin adawa da hakan ke fuskanta a cikin gida da waje.

Kungiyoyin fararen hula da dama a jihar Fukushima, da sauran wuraren kasar sun sanar a wannan rana cewa, mutane 254,000, sun rattaba hannu kan adawa da wannan shirin. Wani binciken hadin gwiwa da kafafen yada labarai na Japan, da Koriya ta Kudu suka gudanar, ya nuna cewa, sama da kashi 80% na al’ummar Koriya ta Kudu, ba su amince da shirin na Japan ba.

  • Sin Ta Bukaci Japan Da Kada Ta Yi Yunkurin Amfani Da Rahoton IAEA A Matsayin Izinin Zubar Da Dagwalon Ruwan Nukiliya A Cikin Teku

Kaza lika jama’a a kasashen tsibiran tekun Pasifik, da Philippines, da Indonesia, da Afirka ta Kudu, da Peru, da sauran kasashe da dama, sun yi korafi game da wannan batu a ’yan kwanakin nan. Hakan na nuni da cewa, matakin da kasar Japan ta dauka na zubar da dagwalon ruwan nukiliya a cikin teku, wanda ya saba wa ra’ayin al’ummar duniya, bai samu amincewa ba.

ADVERTISEMENT

Bugu da kari, sakamakon wasu kuri’un jin ra’ayin al’umma guda 2 da kafar CGTN ta gudanar ta yanar gizo sun nuna cewa, kaso 94.85 bisa dari na wadanda suka amsa tambayoyi sun yi Allah wadai da matakin kasar Japan, suna masu bayyana shi a matsayin tsananin rashin sanin ya kamata, kana karin wasu kaso 3.64 bisa dari kwatankwacin na watanni 3 da suka gabata. Yanzu haka dai sassan kasashen duniya na ta kara nuna damuwa ga matakin da Japan din ke burin aiwatarwa.

Wannan bincike, wanda kafar CGTN ta fitar ta tashoshin ta na Turanci, da Faransanci da Larabci, da yarukan Sipaniya da na Rasha, ya samu amsoshi daga mutane kusan 34,000 cikin sa’o’i 24.

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Domin tsimin kudi, Japan tana daukar tekun Pasifik a matsayin magudanar ruwa, wanda hakan zai rataya mata diyyar kasashen duniya ta fuskokin da’a da sanin ya kamata.

Idan har Japan ta dage sai ta zubar da dagwalon ruwan nukiliyar ta cikin teku, to tabbas hakan zai sanya ta jin kunya ta tsawon tarihi. (Masu Fassarawa: Bilkisu Xin, Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya
Daga Birnin Sin

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Daga Birnin Sin

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Next Post
Sharhi: Sin Da Amurka Ba Su Bukatar Zama Abokan Gabar Juna 

Sharhi: Sin Da Amurka Ba Su Bukatar Zama Abokan Gabar Juna 

LABARAI MASU NASABA

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Hallaka Dama-Dama

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Hallaka Dama-Dama

November 15, 2025
Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

November 15, 2025
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025
Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

November 15, 2025
Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.